Ma’aikatan gidan namun daji na Adelaide da ke ƙasar Ostiraliya sun bayyana farin cikinsu bayan wata tsuntsuwa mai suna Southern Cassowary ta yi ƙwai biyu masu launin kore mai haske, a karon farko cikin shekaru 34 da gidan namun dajin ya yi ba tare da samun irin waɗannan ƙwayayen ba.
Tsuntsuwar mai shekara 10, mai suna Martina, ta yi ƙwayayen ne bayan an haɗa ta da wani namijin tsuntsu mai shekara 13 mai suna Jeffrey, da nufin su hayayyafa.
ƙwayayen wannan nau’in tsuntsu suna da launin kore mai haske, wanda ke taimaka musu wajen ɓoyuwa a cikin ciyayi da ganyayen daji, domin kare su daga mafarauta.
Sai dai, ma’aikatan gidan namun dajin sun bayyana cewa har yanzu ba su tabbatar ko ƙwayayen suna da ikon ƙyanƙyashewa ba. Hakan na nufin ba a san ko za a samu ƙananan tsuntsaye daga cikinsu ba.
Wani abin ban sha’awa game da wannan nau’in tsuntsu shi ne, namiji ne yake da alhakin ƙyanƙyashe ƙwai da kuma kula da ’ya’yan bayan sun fito. Wannan ya bambanta da wasu nau’o’in tsuntsaye da mace ke taka muhimmiyar rawa wajen kula da ƙwayayensu.
Lamarin ya zama abin farin ciki ga gidan namun dajin, kasancewar an daɗe ba a samu irin wannan haihuwa ba. Masana na ganin cewa samun ƙwai wani muhimmin mataki ne a ƙoƙarin kula da wannan nau’in tsuntsu da tabbatar da ci gaba da samuwarsa.
Southern Cassowary na daga cikin manyan tsuntsayen da ba sa iya tashi sama, kuma sun fi zama a dazuzzukan yankin Ostiraliya da wasu sassan ƙasashen da ke kusa da ita. An san su da ƙaƙƙarfan jiki, dogayen ƙafafu da kuma wani irin ƙaho mai kama da hular ƙashi a saman kai.
Masu kula da namun daji na ci gaba da sa ido kan ƙwayayen, domin gano ko za su ƙyanƙyashe, wanda hakan zai zama wata babbar nasara ga gidan namun dajin na Adelaide.
