Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Babbar Kotun Jihar Gombe mai lamba ta tara ta tabbatar da cewa kamfanin Emir General Integrated Ltd ne halastaccen mamallakin wani fili mai faɗin hekta 1.30 da ke kan titin Gombe–Bajoga a ƙaramar hukumar Gombe, tare da bai wa kamfanin diyyar Naira miliyan 65 bayan ta gano cewa an kutsa masa tare da rusa kadarorinsa ba bisa ƙa’ida ba.
Mai shari’a Daurabo S. Sikkam ce ta yanke hukuncin a shari’a mai lamba GM/116/2026, inda ta tabbatar da cewa takardar mallakar fili (Certificate of Occupancy) mai lamba GM/15926 da kamfanin ke da ita tana nan da cikakken inganci a idon doka.
Waɗanda aka shigar ƙarar sun haɗa da Grandscope Construction Ltd, Gwamnatin Jihar Gombe, Babban Lauyan Jihar Gombe da kuma kwamishinan ma’aikatar ayyuka, gidaje da sufuri.
Filin da ake taƙaddama a kansa yana kusa da ofishin ƙungiyar direbobin mota ta ƙasa (NURTW) da ke kan titin Gombe–Bajoga. Da aka mayar gandun makanikai wato Mechanic village
Kotun ta bayyana cewa matakin gwamnatin jihar na bai wa kamfanin Grandscope Construction Ltd kwangilar gudanar da aiki a filin, wanda ya haddasa rusa gine-ginen kamfanin da kuma ci gaba da wasu ayyukan gini ba tare da bin ƙa’idojin doka ba, ya saɓa wa doka kuma kutse ne a kan kadarorin kamfanin.
Saboda haka, kotun ta haramta wa waɗanda aka yi ƙarar, wakilansu da duk masu aiki a madadinsu ci gaba da shiga ko tsoma baki a filin.
Har ila yau, kotun ta umarce su da su rushe tare da kwashe duk wasu gine-gine da kayayyakin da suka kafa a filin.
Bugu da ƙari, kotun ta bai wa kamfanin Emir General Integrated Ltd diyyar musamman ta Naira miliyan 15 da kuma diyyar gaba ɗaya ta Naira miliyan 50, wanda ya kai jimillar Naira miliyan 65.
Haka kuma ta ba shi kuɗin shari’a na Naira 7,200, tare da umartar cewa kuɗaɗen da aka yanke za su riƙa karɓar ribar kashi 10 cikin 100 a duk shekara har sai an biya su gaba ɗaya.
Da yake bayyana ra’ayinsa bayan yanke hukuncin, lauyan kamfanin, Barrista Sulaiman Abdurrahim, ya ce hukuncin ya tabbatar da cewa doka tana kare haƙƙin kowane ɗan ƙasa.
Ya bayyana cewa dokar amfani da fili (Land Use Act) ta wajabta wa gwamnati sanar da mamallakin fili tare da biyansa diyya idan tana son karɓe filinsa domin amfanin jama’a, musamman idan yana da ingantacciyar takardar mallakar fili.
A cewarsa, gwamnatin jihar ba ta bi wannan tanadi ba, duk da cewa kamfanin yana da ingantacciyar takardar mallaka, sannan ta ci gaba da aiki duk da umarnin kotu guda biyu da suka hana yin hakan.
Barrista Abdurrahim ya yi kira ga Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya da gwamnatin jihar su mutunta hukuncin kotun ta hanyar biyan diyyar da aka yanke da kuma miƙa filin ga kamfanin kamar yadda kotu ta umarta.
Wakilin mu ya ruwaito cewa babu lauyoyin da ke wakiltar Grandscope Construction Ltd, Gwamnatin Jihar Gombe, ma’aikatar ayyuka, gidaje da sufuri da kuma babban lauyan Jihar da suka halarci zaman kotun lokacin da aka yanke hukuncin.
