Amurka da Iran sun yi musayar wuta a mashigar Hormuz

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kasar Iran ta ce ta ƙaddamar da hare-hare akan wasu manyan jiragen dakon mai a yankin mashigar Hormuz da ke gaɓar ruwan iyakarta

Dakarun juyin juya halin Musulunci na Iran sun ce suna kai hare-hare kan ne akan jiragen da kuma wuraren da ke da alaƙa da Amurka a ƙasar Bahrain, yayin da rikici a tsakanin ƙasashen biyu ya sake caɓewa.

Dakarun sun ce, sun lalata wasu jiragen ruwan dakon mai bayan sun yi watsi da gargaɗin da aka yi musu tare da kashe na’urorin da ke nuna inda suke zirga-zirga.

A nata ɓangaren, rundunar sojin Amurka ta ce dakarunta sun kai hare-hare akan wuraren da sojoji suke a sassan Iran.

Rundunar ta kuma ce a yanzu Amurka tana da sojoji guda 50,00 da aka jibge a yankin Gabas ta Tsakiya.

By Babaji

Leave a Reply