Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Marigayi Dokta Musa ɗankwairo Maradun ya ce Shehu 3 ag ga Nijeriya Shehu Sakkwato da Shehun Borno sai marigayi Shehu Usman Abubakar na Gombe. A nan kan Shehu na farko da na biyu na ke magana ko ma dai kai tsaye Daular Sokoto da Daular Borno. Wadannan biyun dauloli biyu ne da a ka yi a yankin Arewa da kewaye kuma na addinin musulunci. Duk da zuwan Turawa ya sauya tarihinsu amma har gobe tasirinsu na nan daram. Ba abun da ya ƙarfafa tasirin sai bin tsarin addinin Musulunci wajen ibada da kyautatawa kowa da Musulmi da wanda ba Musulmi ba. Wacannan dauloli sun sha fuskantar farmaki hatta ma bayan tafiyar Turawa da su ka kafa sabon tsari da ya sauya masarautun. Babbar alamar masarautun shi ne fadar Sarki mai kallon yamma da kuma masallaci mai kallon alƙibla ko gabar kamar yadda za a fi ganewa. Da zarar mutum ya shiga manyan biranen daulolin zai ga sauran tsarin da iyaye da su ka kafa su su ka bari na ginshiki mai ƙarfi kuma wanda da yardar Allah zai wanzu har zuwa ƙarshen rayuwa. Mai adawa da tsarin shi ne wanda ba ya son zaman lafiya da nagartattun al’adu sabanin zamanin jahiliyya.
Kamar yadda Gudumar wakilin tarihin Daura ta tarwatsa makircin Zallawa masu shigar burtu a matsayin Hausawa don yaki da Musulunci, su ma ‘yan uwa Barebari su dauko Yasin mai fuka-fuki su fantsamawa wasu Zallawan Kanuri da su ka bayyana don kawo ruɗanin ƙabilanci a Daular Kanem Bornu.
A gurguje na ga sun fara sakar da mugun zare don buƙatar Kanuri su daina amfani da sunayen Musulunci su koma na Kanuri irin Kime, Modu, Kyari, Ari, Fanna, Falmata da sauran su. Wato su yi watsi da Ibrahim, Musa, Abubakar, Umar da sauran sunaye masu daraja ga Musulmi.
Zallawan na Kanuri sun yi iƙirarin wai wani ɗan Izala ne ya ribaci wasu su ka canja sunan Kanuri zuwa IBRAHIM don haka su ke ba da shawarar a rika bambance addinin Musulunci, Harshen Larabci da sunayen Larabawa.
Kamar dai yadda ‘yan barandar AIFOB na Arewa ke fara cewa su Musulmi ne amma su tsula tsiya, haka ma Zallawan Kanuri su ka yi iƙirari da nuna ai ba ayar da ta hana amfani da sunayen gargajiya na Kanuri. A nan ba su kuma kawo ayar da ta hana Kanuri amfani da sunayen Musulunci ko na Larabawa da su ke turewa ba.
Na ga wani mai ilimi ya ja hankalinsu cewa sunan Ibrahim ma ba na Larabawa ba ne amma na uban Annabawa ne Annabi Ibrahim Alaihis salam. Kazalika na ga wani ma ya rubuta tun kafin a kafa Izala ai a na amfani da sunan Ibrahim don in an duba hatta Shaihul Islam Ibarhim Niasse sunansa kenan ga Kuma Sheikh Ibrahim Yakub Elzakzaky. A nan sunan IBRAHIM ba maganar Izala, ɗarika ko Shi’a ba ne, a’a sunan babban Annabin Allah ne baban Annabawa.
Wautar wannan hannun da na hango hayaƙin Kafaru da AIFOB sun manta an yi shahararren shugaban Amurka na 16 mai suna IBRAHIM wato Abraham Lincoln.
KANURI KU ZUBA IDO kar nan gaba wani ya ce ku kori sauran ƙabilu a yankinku, ku farfado da al’adun Kanuri tsantsa maimakon na Larabawa! Da kun ji sun ce Larabawa to Musulunci su ke nufi kamar yadda ‘yan karyar Hausa zalla ke cewa Fulani alhali Musulunci su ke kai wa farmaki a kaikaice.
Tabbas buyan da Zallawa ke yi da turo wasu ‘yan figaggun mutane su na surutai na rashin sanin inda Hausa da Arewa su ka dosa, na nuna tsananin tsoron sakamakon da za a samu. Mutum ne ya daure rago sai ya dawo ya ga kare a daure jikin tirke, kai ka san an kawar da ragon an kawo wanda ba ya layya.
Zallawan nan sun san ba Hausawa ba ne kuma ba mabiya tauhidi ba ne don haka su ke buya kar a gansu tsirara rago da fatar kare.
Yo in ma ba shakiyanci ba, ta yaya wanda don tsoro ya ɓoye suna da hoto da adireshi ya na dankwalo a duhu zai iya shafe tasirin Musulunci a Arewa. Ai da na gaba kan gane zurfin ruwa sai su duba tarihin yadda mai jan kunne ma ya shigo da ruwan albarusai ya kashe ya danne ya ƙone, amma haka rana tsaka ya koma ƙasarsa ba tare da cimma muradi ba.
Ai duk wanda ya ce zai gyara tsayuwar wata sai ya hau sama ya gwada. Fir’auna ma don jabbaranci ya buƙaci Hamana ya shirya ma sa tsani don hawa sama ya yi yaki da ubangijin sammai da ƙassai. Ko a nan ai akwai gazawa don ya nuna sai ya hau tsani ya samu wanda ke sama da shi nan ma maimakon ya daka tsalle sai ya hau kuranga!.
To gara ma waɗancan a fili su ke amma ina ga wanda a ka ba wa kwangila ya buya a salula ya na murɗe wuyan tarihi da shirga karya don ingiza musulmi su hau ɗauki ba daɗi da juna? Wannan tamkar shiga maliya da yasa ne.
Kullum ƙalubalen shi ne in mutanen nan da gaske su ke yi su bayyana kansu a ga su waye, ma’ana dukkansu su fito fili su daina ɓuya. Mai zunduma ashar zundum a boye ya fito fili ma na a yi ta, ta kare. In da ba kasa a ke gardamar kokawa.
Haka mu ke gani kullum in hujja ta yi hujja an kure Bazalle ya shiga can kuryar kwana, sai ya waigo ya zuduma ashar zundum don shi ne tasbihin Kadamusawa.
Kazalika in Bazalle ya gaji da ashar sai ya wurgo hoto ko bidiyon ‘yan uwansa na daji don cika aikin kwangila.
Wallahi duk mai cewa an danne Hausawa ya dace a rufe bakinsa don tantirin makiri ne mai neman kawo fitina a cikin al’ummar Arewa. Ko ina harkar Bahaushe da Hausawa a ke yi a Arewa hatta wannan rubutun da na ke yi.
Haba wa Midiblewa da ‘yan AIFOB za su yaudara da basaja don kammala wargaza Arewa. Iyayen Arewa ƙarƙashin Shehu Mujaddadi sun feshe Arewa da addu’ar albarka da neman kariyar Allah daga makircin Zallawa.
Yaushe mai gaskiya zai buya a wayar salula ya na zuba bayanai wai kuma lallai sai a yarda da maganarsa a watsar da ta wanda ya ke sananne kuma a fili tarwal? An yi walkiya.
Lokaci ya yi da duk Zallawa makiya Hausawa za su gane dubunsu ya kusa cika ko su tuba su watsar da kwangilar nan ko su yabawa aya zaki.
Kamfen ɗin Zallawa ya koma nuna ai yanzu kawo batun Musulunci tsohon ya yi ne wai Hausawan zamanin yau sun waye. Fadar Allah ya ce Annabi ya ce tamkar yaudara ce a wajen farafagandar Zallawa.
In da za ka gane m!yagun nan ba masu KALLON GABAR BA NE shi ne ba su taɓa zagin wanda ba Musulmi ba. Duk tafiyarsu malaman Musulunci ne mugaye!.
Dama na sha haska mu ku yadda Zallawa ke fakewa da cewa su Hausawa ne alhali sam ba wata alaƙa da Hausawa sai don wannan kwangila ta cimmawa IPOB da Midibelawa burinsu na aware.
Mutanen nan nan sun fara da zagin Shehu Mujaddadi da dukkan malaman addinin musulunci har su ke ganin kamar sun gama mannawa mutanen masu daraja bakin fenti, yanzu sun buɗe kafa ta aibata Manzon Allah mai tsira da aminci. In wani abokin burminsu na IPOB ya aibata Manzon Allah sai su kawar da kai kamar ba su gani ba amma can gaba in a ka faɗi wani abu na jan hankalinsu sai su jefa shubuha ko baƙar magana su wuce.
Kama daga Zallawa a nan Arewa da iyayen gidansu na IPOB na haduwa yanzu su wuni su na cin zarafin Musulunci. Babban burin shi ne kawar da wadanda su ke ganin matasan Arewa ne daga bin koyarwar gaskiya ta addini da juya mu su akala zuwa bijirewa limamai da sauran malaman Musulunci.
Idan ‘yan Arewa Musulmi su ka cauka Musulunci ya zama tsohon ya yi, shikenan maƙiya sun samu hanyar wargaza yankin a siyasance, al’adance da tattalin arziki. Daga nan a bulus za a kafa Biyafara da kuma barin miyagu na Midil bel su ci karensu ba babbaka.
KAMMALAWA
Duk mabiyin addinin Kirista na kwarai musamman a nan Arewa ba ya tsokanar Musulmi kuma ba ya giggiwar aibata Manzon Allah mai tsira da aminci. Kai ko Zallawan nan su kan yi takatsantsan wajen aibata Manzon Allah ko zagin musulunci, sai dai su fake da cewa addinin FULAKU ko FODIYANCI da sauran sharrin da su ka ƙirƙiro da gangan don samun damar dirar miƙiya kan musulmi ta bayan fage. An wayi gari Zallawa na fitowa farafaganda da taron gayyar madugun ‘yan aware da ke ɗaure a Sokoto. Zallawan Aware kan yi martani da wauta don ba su da hankali kuma ba su nakalci yadda fakihun Arewa ya ke ba sai ta kankambar soshiyal midiya.
Na sha haska mu ku gaggan karambanannu a mutanen nan ba musulmi ba ne amma sun mannewa Musulunci don ingiza Hausawa su shiga ɗauki ba daɗi da juna a doron kabilanci. Ba kun ga zugar da su ke wai akwai wasu limamai Fulani ko malamai Fulani a daina bin su sallah ko a daina sauraron wa’azinsu. Ai makircin ya samu cikas ne don musulmi na miƙa wuya ne ga Allah da shaidawa Annabi Muhammadu SAW manzon Allah ne. Ba batun kabilanci sam. Da zarar an tsaida sahun sallah kowa Allah ya ke tunawa ba ƙabilar liman ba.
