Daga UMAR GARBA a Katsina
Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika, ya bayyana cewa marigayi tsohon Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bar Nijeriya cikin yanayi na ci gaba, tare da ingantaccen tattalin arziki da tsaro mai kyau.
Da yake magana a tashar ARISE TV, Sirika ya ce gwamnatin Buhari ta gaji matsaloli masu yawa, amma ta samu nasarori wajen yaƙi da Boko Haram, inda ta ƙwato ƙananan hukumomi 17 da ‘yan ta’adda suka mamaye tare da ceto wasu daga cikin ɗaliban Chibok da aka sace.
Ya kuma ce inganta tsaro ya bai wa al’umma damar komawa noma, zuwa makarantu da kuma zirga-zirga cikin kwanciyar hankali.
Game da tattalin arziki, Sirika ya ce Buhari ya bar ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje mai ƙarfi da kuma yanayin da ya ba kamfanoni da masu kasuwanci damar bunƙasa.
Sai dai ya guji sukar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa gwamnatocin Buhari da Tinubu duk suna aiwatar da manufofin jam’iyyar APC ne domin amfanin ƙasa.
Kazalika, Sirika ya kare shirin bayar da filayen jiragen sama na Lagos, Abuja, Fatakwal da Kano ga kamfanoni masu zaman kansu, yana mai cewa an gudanar da tsarin cikin gaskiya da cikakken bin doka kafin shari’a ta dakatar da aiwatar da shi.
