
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja, ta jaddada hukuncin haramta wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) amincewa ko karɓar kowane babban taro da shugabancin jam’iyyar ADC na tsagin su David Mark ya jagoranta.
A wani zama da kotun ta gudanar a ranar Litinin, ta sake jaddada hukuncin Babbar Kotun Tarayya da aka gudanar a ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Joyce Abdulmalik a Abuja.
Hukuncin, wanda aka gabatar a ranar 29 ga watan Afrilun 2026, ya haramta wa INEC tabbatarwa ko karɓar kowane ɗaya daga cikin tarukan ƙasa da shugabancin David Mark ya jagoranta daga ɓangaren jam’iyyar adawar.
Wannan ya nuna cewa, Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta ƙarfafa dokar da ta gindaya wa INEC na hana ta karɓar kowane babban taro na ADC da aka gudanar a ƙarƙashin tsohon Shugaban Majalisar Dattawan.
Biyu daga cikin alƙalan da suka jagoranci zaman, sun tabbatar da hukuncin Mai Shari’a Joyce Abdulmalik yayin ɗaya daga ciki ya ƙi bin su akan matakin.
