Bilkisu Yusuf: Matar da ta rusa katangar da ke hana mata jagorantar ɗakunan labarai

Spread the love

“Ba ta rubutu don faranta wa masu mulki, kuma ba ta rubutu don ta jawo cece-kuce”

A tarihin Nijeriya, akwai wasu mata da ba a auna darajarsu da mukaman da suka riƙa ko lambobin yabo da suka tara. Ana ci gaba da tuna su ne saboda irin sauyin da suka kawo a rayuwar al’umma da kuma kyawawan abubuwan da suka bari a baya.

Shafin Gimbiya na wannan makon ya zaƙulo ɗaya daga cikin irin waɗannan fitattun mata, wato Bilkisu Yusuf; mace mai hangen nesa, ƙwararriyar ‘yar jarida, gogaggiyar edita kuma fitacciyar mai fafutukar tabbatar da adalci da ci gaban al’umma. Idan kuwa ba ita ce ta cancanci a kira Gimbiya ba, to wacce mace ce ta fi dacewa da wannan kirari?

A lokacin da shugabancin ɗakunan editocin jaridu ya kasance kusan mallakin maza kaɗai, Bilkisu Yusuf ta fito da ƙwarewa, jajircewa da ƙwazon aiki, inda ta karya wannan katanga tare da tabbatar da cewa ƙwarewa ba ta da alaƙa da jinsi. Sunanta ya zama alamar gaskiya, riƙon amana da ƙwazon aiki, yayin da dubban matasa, musamman mata masu sha’awar aikin jarida, inda suka fara kallon ta a matsayin abin koyi.

Sai dai abin da ya fi bambanta Bilkisu Yusuf da sauran fitattun ‘yan jarida shi ne cewa tasirinta bai tsaya a cikin ɗakin labarai kaɗai ba. Ta fahimci cewa aikin jarida ba sana’ar rubuta labarai kawai ba ce, hanya ce ta gina al’umma, kare muradun talakawa da kuma tunasar da masu mulki nauyin da ke kansu. Wannan fahimta ce ta sa ta shiga kusan duk wata fafutuka da ta shafi ilimi, kare haƙƙin mata, dimokuraɗiyya, zaman lafiya da haɗin kan addinai.

MANHAJA: Wace ce Bilkisu Yusuf?

An haifi Bilkisu Yusuf a ranar 2 ga Disamban shekarar 1952 a birnin Kano. Duk da cewa iyayenta sun fito ne daga zuriyar Yarbawa da suka daɗe suna zaune a Arewacin Najeriya, rayuwarta ta kasance cikin al’adun Hausawa, al’ummar da ta yi alfahari da kasancewa cikinta. Ta taso cikin tarbiyyar addinin Musulunci, wadda ta zame mata ginshiƙin tafiyar da rayuwarta da aikinta.

Tun tana ƙarama ta nuna ƙwazo wajen neman ilimi. Ta fara karatunta a Makarantar Ansar Primary School da ke Kano, inda ta kammala a shekarar 1964. Daga nan ta wuce Government Girls College da ke Dala, ɗaya daga cikin fitattun makarantun mata a Arewacin Najeriya. A can ne aka fara lura da irin hazaka da ƙwarewar da take da ita wajen nazari da bayyana ra’ayi.

Da ta shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ta zaɓi karantar Kimiyyar Siyasa. Wannan fanni ya buɗe mata ƙofofin fahimtar shugabanci, tsarin mulki da yadda rayuwar al’umma ke tafiya. Sai dai ƙishinta na neman ilimi bai tsaya nan ba.

Bayan kammala digirinta na farko, ta tafi Amurka inda ta samu digiri na biyu a fannin Kimiyyar Siyasa da Harkokin ƙasa da ƙasa daga Jami’ar Wisconsin-Madison. Wannan karatu ya ƙara faɗaɗa mata tunani tare da ba ta damar fahimtar yadda ƙasashe daban-daban ke tafiyar da al’amuransu.

A shekarar 1986 kuma ta ƙara zurfafa ƙwarewarta a aikin jarida bayan ta halarci Cibiyar Koyar da Aikin Jarida ta Moscow State Institute of International Relations a tsohuwar Tarayyar Soviet. Wannan horo ya haɗa ilimin siyasar da ta samu da ƙwarewar aikin jarida, abin da ya sa ta fara kallon aikin jarida a matsayin wata babbar hanya ta kawo sauyi a rayuwar al’umma.

Da ta dawo Najeriya, ba ta daɗe ba ta fara jan hankali a gidajen jaridu. Rubuce-rubucenta sun bambanta da na wasu saboda zurfin bincike, daidaiton hukunci da kuma kauce wa son zuciya. Ba ta rubuta don faranta wa masu mulki rai ba, haka kuma ba ta rubutu don ta jawo cece-kuce ba. Burinta shi ne gaskiya ta fito fili, jama’a kuma su samu bayanan da za su taimaka musu wajen fahimtar al’amuran ƙasa.

Wannan ƙwarewa ce ta kai ta ga kafa tarihi bayan da aka naɗa ta Editar jaridar Sunday Triumph a Kano. Wannan naɗi ya zama wani sabon babi a tarihin aikin jarida a Najeriya, domin ita ce mace ta farko da ta jagoranci editocin wannan jarida. A lokacin da ake kallon shugabancin ɗakunan labarai a matsayin aikin maza, Bilkisu Yusuf ta tabbatar da cewa ƙwarewa, jajircewa da nagarta ne ginshiƙan jagoranci.

Nasarar da ta samu ba ta amfani kanta kaɗai ba. Ta zama ƙofa da ta buɗe wa mata masu sha’awar aikin jarida damar yin mafarkin kaiwa matakin jagoranci. Tun daga wannan lokaci, sunanta ya shiga sahun fitattun ‘yan jaridar da ake kallo da girmamawa a Najeriya.

Amma Bilkisu Yusuf ba ta taɓa ɗaukar wannan matsayi a matsayin ƙarshen tafiyarta ba. A gare ta, wannan shi ne farkon wata babbar tafiya ta hidimar ƙasa, tafiyar da ta kai ta zama ɗaya daga cikin fitattun mata masu tasiri a tarihin aikin jarida da ƙungiyoyin fararen hula a Najeriya. 

Lokacin da aikin jarida ya zama makamin gyaran al’umma:

Bayan nasarar da ta samu a Sunday Triumph, Bilkisu Yusuf ta ci gaba da taka matakan da ba mata da yawa ne suka kai ba a wancan lokacin. An naɗa ta Editar jaridar New Nigerian da ke Kaduna, ɗaya daga cikin manyan jaridun da suka taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar muhawarar siyasa da zamantakewar Najeriya. Daga nan kuma ta jagoranci Citizen Magazine, inda ta ci gaba da nuna ƙwarewarta wajen tsara manufofin editoci da tabbatar da cewa aikin jarida ya kasance mai kare muradun jama’a.

Sai dai duk inda ta yi aiki, ba muƙami ne ya fi jan hankalinta ba. Abin da ya fi damunta shi ne yadda jarida za ta kasance muryar waɗanda ba su da damar a ji su. Ta yi imanin cewa ɗan jarida ba mai ba da labari kawai ba ne, mutum ne da ke da alhakin taimaka wa al’umma ta fahimci gaskiyar abin da ke faruwa a cikinta.

Daga baya ta yi aiki da jaridun Daily Trust da Leadership, inda ta ci gaba da rubuce-rubuce masu zurfi kan shugabanci, dimokuraɗiyya, ci gaban ƙasa da kuma rawar da ƙungiyoyin fararen hula ke takawa wajen tabbatar da shugabanci nagari. Rubuce-rubucenta sun kasance masu cike da hujjoji da nutsuwa, ba tare da karkata ga wani ɓangare ko amfani da kalaman da za su iya rura wutar rikici ba.

ɗaya daga cikin rubuce-rubucenta da suka fi shahara shi ne maƙalarta mai suna ‘Civil Society Watch’. Wannan shafi ya zama wata muhimmiyar kafa ta tattauna manyan batutuwan ƙasa. A cikinsa, Bilkisu Yusuf ba ta tsaya ga bayyana matsaloli kawai ba; tana nazartar tushensu tare da gabatar da hanyoyin magance su. Ta kasance cikin marubutan da suka yi imanin cewa sukar gwamnati ba ta cika amfani ba idan ba a haɗa ta da shawarwari masu ma’ana ba.

Salon rubutunta ya sa aka fara kallonta a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu sharhi kan al’amuran ƙasa. Ko masu ra’ayin da ya bambanta da nata suna girmama yadda take gabatar da hujjoji cikin ladabi tare da mutunta ra’ayin wasu.

Sai kuma wata gudunmawa mai matuƙar muhimmanci wadda ba kasafai ake ba ta kulawar da ta dace ba, ita ce yadda ta yi amfani da matsayinta wajen renon sababbin ‘yan jarida. Ta fahimci cewa makomar aikin jarida tana hannun matasa, musamman mata da ke shiga wannan sana’a a lokacin da har yanzu ake kallonta a matsayin fannin da aka fi dangantawa da maza.

Ta hanyar ƙungiyar Mata ‘Yan Jarida ta Najeriya, ta ba wa matasa shawara, ta horas da su, tare da ƙarfafa musu gwiwar cewa ƙwarewa da riƙon amana su ne manyan ginshiƙan samun nasara. Saboda haka, mata da dama da ke cikin fitattun editoci da marubuta a yau suna ambatonta a matsayin wadda ta ƙarfafa musu gwiwar ci gaba da wannan sana’a, wadda ita kanta ta ɗauka a matsayin hidima ga al’umma.

Duk da irin waɗannan gudunmawa, Bilkisu Yusuf ba ta taƙaita kanta ga aikin jarida kaɗai ba. Ta yi amanna da cewa idan ana son samun sauyi na gaskiya, dole ne a haɗa aikin jarida da ayyukan raya al’umma. Wannan tunani ne ya sa ta shiga cikin ƙungiyoyi da dama masu fafutukar kawo ci gaba.

Ta kasance cikin mutanen farko da suka kafa ‘Women in Nigeria’, ƙungiyar da ta taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan al’umma game da haƙƙin mata da daidaito tsakanin maza da mata. A lokacin da irin waɗannan batutuwa ba su samu karɓuwa sosai ba, Bilkisu Yusuf ta yi amfani da iliminta da ƙwarewarta wajen nuna cewa ci gaban ƙasa ba zai tabbata ba idan aka bar rabin al’umma a baya.

Haka kuma ta kasance cikin fitattun jagororin ‘Federation of Muslim Women’s Associations in Nigeria’ (FOMWAN). Ta yi aiki tare da wannan babbar ƙungiyar matan Musulmi wajen inganta ilimi, kiwon lafiya da bunƙasa rayuwar al’umma. A gare ta, addini ba ibada kawai ba ne; hanya ce ta yi wa mutane hidima da sauƙaƙa musu rayuwa.

Ayyukanta sun kuma kai ta zuwa ƙungiyoyin da ke yaƙi da cutar zazzabin cizon sauro da kuma fafutukar inganta tsarin kiwon lafiya. Ta taka muhimmiyar rawa a ‘Nigerian Interfaith Action Association Against Malaria’ da kuma ‘Health Reform Foundation of Nigeria’, inda ta yi aiki tare da masana da sauran masu ruwa da tsaki domin nemo hanyoyin inganta lafiyar jama’a.

A matsayinta na Babbar Daraktar Advocacy Nigeria, ta jagoranci shirye-shiryen da suka shafi shugabanci nagari, ci gaban jama’a da kare lafiyar al’umma. Duk waɗannan ayyuka sun nuna cewa, a gare ta, aikin jarida ba ya ƙarewa da buga labari. A ganinta, ya kamata ya zama wata hanya ta haifar da sauyi da ci gaba.

A shekarar 2014, lokacin da aka sace ɗaliban makarantar Chibok, Bilkisu Yusuf ta shiga sahun masu neman a dawo da ‘yan matan gida lafiya. Ta mara wa ƙungiyar ‘Bring Back Our Girls’ baya, tare da yin kira ga gwamnati da kuma duniya baki ɗaya da kada su manta da makomar waɗannan yara mata.

A fahimtarta, ilimi shi ne ginshiƙin ci gaban kowace al’umma. Saboda haka, duk wani hari da ake kai wa makarantu ko hana yara, musamman mata, samun ilimi, barazana ce ga makomar ƙasa bakiɗaya.

Labarin Gimbiya Bilkisu Yusuf bai tsaya nan kaɗai ba. Sai dai ƙayyadadden adadin kalmomin wannan shafi ne ya sa muka saka aya a nan. Da yardar Allah, a mako mai zuwa masu karatu za su ci gaba da karanta ƙarin bayani kan muƙaman da ta riƙa da kuma yadda ta yi amfani da aikin jarida wajen hidimtawa al’umma da ƙasarta bakiɗaya.

By ukarofi

Leave a Reply