Yawancin mutanen Amurka suna rayuwar hannu-baka-hannu-ƙwarya, inji mazaunin ƙasar

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wani ɗan kasuwar Nijeriya kuma mai harkar bunƙasa gidaje da ke zaune a Amurka, Femi Rogers, ya yi kira ga matasan Nijeriya da ke kallon ƙaura zuwa ƙasashen waje a matsayin mafita ta samun sauƙin rayuwa da su sake nazari, yana mai cewa rayuwa a Amurka ba ta da sauƙin kuɗi kamar yadda mutane da dama ke zato.

Rogers ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin Frankly Business Podcast, inda ya ce tsadar gidaje, haraji, kuɗin wutar lantarki, ruwa da sauran kuɗaɗen rayuwa na sanya mutane da dama a Amurka rayuwa daga abin da suka samu zuwa wani, ba tare da samun damar tara kuɗi ba.

A cewarsa, kuɗin haya kaɗai na cin kaso mai yawa daga albashin ma’aikata, inda ya ce haya ta ɗaki ko gida mai sauƙi kan kai tsakanin dala 1,500 zuwa 1,800 a kowane wata.

“Rayuwa a Amurka tana da matuƙar wahala. Gida marar wani inganci ma yana kai tsakanin dala 1,500 zuwa 1,800 a wata. Wannan ba abu ne mai sauƙin bayyana wa wanda bai taɓa rayuwa a ƙasar ba,” inji shi.

Ya ƙara da cewa, duk da cewa mafi ƙarancin albashi a wasu jihohin Amurka na kusan dala 12 a awa ɗaya, ma’aikata da dama har yanzu suna fuskantar ƙalubale saboda tsadar rayuwa. Rogers ya ce idan mutum ya biya kuɗin haya, haraji, sayen kayan abinci da sauran kuɗaɗen amfani da gida, ba ya rage masa wani abin a zo a gani da zai iya ajiyewa.

“Ko kana karɓar mafi ƙarancin albashi, bayan ka biya haya, haraji da kayan abinci, kusan babu abin da ya rage maka,” inji shi.

Ya kuma bayyana cewa kuɗin wutar lantarki na ƙara nauyin rayuwa, musamman a jihohi irin su Teɗas, inda kuɗin lantarki kan kai tsakanin dala 200 zuwa 300 a lokacin zafi saboda yawan amfani da na’urorin sanyaya ɗaki.

A cewarsa, waɗannan kuɗaɗen da ake kashewa akai-akai na hana mutane da yawa damar tara kuɗi ko taimaka wa iyalansu da abokansu. Rogers ya kuma ƙaryata ra’ayin da ya yi ƙarfi a Nijeriya cewa duk wanda ke zaune a ƙasashen waje yana cikin walwala kuma zai iya turo kuɗi gida a duk lokacin da aka buƙata.

Ya ce, “Ra’ayin cewa duk wanda ke ƙasashen waje zai iya aro ko turo kuɗi cikin sauƙi ba gaskiya ba ne, domin mutane da yawa su kansu suna fama da matsin tattalin arziki.”

Da yake kwatanta yanayin tattalin arziki tsakanin Amurka da Nijeriya, Rogers ya ce akwai mutane da dama a Nijeriya da ke samun kuɗaɗen shiga ba tare da aikin gwamnati ko na kamfani ba, al’amarin da ya ce ba kasafai ake samun irinsa a Amurka ba.

“A Nijeriya akwai mutane da yawa da ba sa aiki kai tsaye amma suna samun kuɗi. Wannan abu ba ya faruwa haka a ƙasashen waje,” inji shi.

Ya bayyana cewa a Amurka, samun kuɗin shiga yana da alaƙa kai-tsaye da aiki, kuma saboda tsadar rayuwa, yawancin abin da ake samu kan ƙare wajen biyan muhimman buƙatu, lamarin da ke sa ra’ayin cewa rayuwa ta fi sauƙi bayan Japa ya zama ba daidai ba a lokuta da dama.

By ukarofi

Leave a Reply