NATO ta zaɓi jiragen leƙen asirin Saab na Sweden, ta yi watsi da tayin Boeing na Amurka

Spread the love

Matakin ya zo ne yayin da Trump ke ci gaba da matsa wa ƙawayen NATO su ƙara kashe kuɗi kan tsaro da kuma sayen makaman Amurka.

ƙungiyar tsaron ƙasashen Arewacin Tekun Atlantika (NATO) ta sanar da wani shiri na kusan dala biliyan 4.5 domin sayen sabbin jiragen leƙen asiri da gargaɗin barazana na GlobalEye, waɗanda kamfanin Saab na ƙasar Sweden ta ƙera. Matakin ya nuna cewa ƙungiyar ta fifita fasahar Sweden kan ta kamfanin Boeing na Amurka wajen maye gurbin tsofaffin jiragen AWACS da suka yi shekaru da dama suna aiki.

Sanarwar ta fito ne a yayin taron ƙasashen NATO da ake gudanarwa a birnin Ankara, inda babban sakataren ƙungiyar, Mark Rutte, ya bayyana cewa sabon tsarin zai ƙarfafa ikon NATO na gano barazana tun kafin ta kai ga kai hari, musamman irin sabbin barazanar da jiragen yaƙi marasa matuƙa ke haifarwa.

By ukarofi

Leave a Reply