Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Rahotanni daga garin Sifawa a ƙaramar hukumar Bodinga da ke jihar Sokoto sun bayyana cewa yan bindiga da dama sun mutu yayin da sojoji biyu suka sami raunuka a wani artabu tsakanin sojoji da yan bindiga safiyar Laraba ɗin nan.
Wani ganau ya labartawa wakilin Jaridar Blueprint Manhaja da cewa ana hasashen maharan sun taso ne daga maɓoyar su da ke jejin ƙauyen Horo a karamar hukumar Shagari da zummar mamayar wata ƙaramar barikin sojoji da ke garin Sifawa sai dai ko da suka kunno kai suka tarar sojojin suna cikin shirin ko ta kwana inda aka yi ta ba ta kashi har dai sojojin suka fi karfin su suka kashe waɗansu saura suka gudu.
Yanzu haka dai an girke sojoji da yan sanda jiran ko ta kwana a kan wannan babbar hanyar da ta haɗa jihohin Sokoto da Kebbi da Neja zuwa kudancin ƙasar nan.
Wani direba da ke sufuri a kan wannan babbar hanyar ya bayyana cewa wannan hanyar dai ita ce ɗaya tilo a yankin Arewa maso yamma da ta rage da a ke iya tafiya ba tare da wani shakku ba ko cikin dare yanzu kam dole kowa ya shiga taitayin sa in dai waɗannan ‘yan bindigar za su iya fitowa da rana ƙarara su tinkari barikin sojoji kuma a dauki tsawon lokaci ana bata-kashi.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton babu wani bayani a hukumance dangane da wannan harin sai dai wani jami’in tsaro ya bayyana cewa akwai jami’an sojojin sama da suka bi sawun maharan don idar da kakkaɓe waɗanda suka gudu da ran su duk da ya ke babu tabbacin ko nawa aka kashe daga cikin maharan.
Wata mai kama da wannan, rahotanni daga ƙaramar hukumar Danko Wasagu da ke jihar Kebbi sun tabbatar da cewa wani babban ayari na ƴan bindiga ya yi wa garin zaman-dirshen ƙawanya har na tsawon sama da sa’o’i 24, ba tare da samun ɗaukin jami’an tsaro ba.
Rahotannin sun ce mutane biyu sun rasa rayukansu sakamakon harin wanda aka alkanta shi da nuna tsaurin ido bisa ga umarnin ‘yan bindigar.
An ce sun dai mamaye garin suna kai-komo rariya-rariya rataye da bindigogi a cikin garin.
