‘Yan bindiga sun halaka ɗan uwan ministan Tinubu a Neja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An zargi wasu ‘yan bindiga da halaka wani yayan Ƙaramin Ministan Noma da Tsaron Abinci, Aliyu Sabi Abdullahi a Jihar Neja. Marigayin Mai Gari ne a ƙauyen Galla da ke Masarautar Borgu a Ƙaramar Hukumar Borgu.

A ranar Litinin, 24 ga Agusta, 2026 ne maharan suka afka wa jama’a a fadarsa, lamarin da ya jefa al’ummar ƙauyen cikin firgici.

A cewar rahotanni, majiyoyi masu masaniya kan al’amarin sun ce da fari basaraken ya gargaɗi ‘yan bindiga da su nisanci ƙauyen muddin suna son zaman lafiya. An bayyana wannan gargaɗi a matsayin karan tsaye ga ‘yan ta’adda, waɗanda daga bisani suka koma yankin kuma suka farmake shi.

Wannan al’amari ya tayar da hankalin jama’a a Masarautar Borgu game da halin tsaro da matakin aikata miyagun laifuka da ke ƙaruwa a ‘yan kwanakin nan a yankin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ya ce suna gudanar da bincike kan al’amarin, inda za su fitar da bayanai a kai da zarar sun kammala.

By Babaji

Leave a Reply