Ka daina tsoma baki a idan ‘yan siyasa na magana – Amaechi ga Sowore

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wani fagen tattaunawar harkar siyasa a babban taron Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA) karo na 66 a Fatakwal, Jihar Ribas ya koma cacar baki bayan ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore ya ƙalubalanci tarihin siyasar ‘yan siyasar da suka riƙe muƙaman gwamnati a baya.

Ana haka ne tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi, wanda ya wakilci ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar a taron, ya mayar da martani kan sukar. Ya ƙalubalanci Sowore da ya bayyana ƙwarewarsa a fagen shugabanci.

An fara musayar kalaman ne yayin tattaunawa kan makomar siyasar Nijeriya, cire tallafin fetur, tsarin sufuri da aikin da tsofaffin jami’an gwamnati suka yi gabanin zaɓukan 2027.

Sowore ya ce, akwai buƙatar ‘yan siyasar da suka riƙe muƙaman gwamnati su bayyana nasarorin da suka cimmawa kafin sake neman ‘yan Nijeriya su zaɓe su a matsayin jagorori. Musamman ya ƙalubalanci aikin Amaechi a lokacin da ya riƙe muƙaman gwamnan Ribas da ministan sufuri, da kuma gabatar da maganarsa kai-tsaye ga tsohon gwamnan Jihar Anambara, Peter Obi.

Ya ce, ‘yan siyasar da suka yi shugabanci ba tare da sauke nauyin da suka ɗauka ba bai dace su sake dawowa neman a zaɓe su ba domin riƙe wani muƙami. A yayin haka ne ya caccaki aikin titin jirgin ƙasa da aka bayar a lokacin da Amaechi yake minista, tare da cewa yayin da aka samu tsadar farashin mai, ya dace a samarwa al’umma mafita domin samun sauƙin zirga-zirga.

Saidai, Amaechi ya yi watsi da wannan iƙirari inda ya ce akwai buƙatar a duba ayyukan da ya yi a lokacin a madadin yi masa hukuncin da abin da aka faɗa yayin muhawarar siyasa. Ya bayar da misali da gina titina da makarantu a lokacin da yake gwamnan Ribas da kuma ayyukan layukan dogo da aka aiwatar yayin da yake ministan sufuri a Nijeriya.

By Babaji

Leave a Reply