Yadda ake amfani da kafafen sadarwa na zamani: Tasirinsu, damarmaki da ƙalubale kashi na biyu

Spread the love

Daga BILKISU YUSUF ALI, Ph’D

Gabatarwa:

Kamar yadda muka faro bayani a makon da ya gabata. Kafafen sadarwa na zamani sun zama ginshiƙin sadarwa a ƙarni na 21. Sun sauƙaƙa yaɗa bayanai da ilimi da  kasuwanci da  siyasa da hulɗar jama’a cikin sauri. Duk da haka, rashin amfani da su yadda ya kamata na iya haifar da yaɗuwar labaran ƙarya da zamba ta yanar gizo da cin zarafi da rashin tsaro. Wannan takarda ta yi bayani kan ma’anar kafafen sadarwa na zamani, nau’o’insu, yadda ake amfani da su cikin hikima, fa’idodinsu, ƙalubalen da suke tattare da su, da hanyoyin inganta amfani da su domin ci gaban al’umma. Ci gaban fasahar sadarwa ya canja yadda mutane ke rayuwa da mu’amala. A da ana dogaro ne da wasiƙa da rediyo da talabijin, amma a yau wayoyin hannu da intanet sun bai wa kowa damar isar da saƙo cikin daƙiƙu. Kafafen sada zumunta kamar Facebook da WhatsApp da ɗ (Twitter) da  Instagram da  TikTok da YouTube sun zama muhimman hanyoyin sadarwa tsakanin mutane da gwamnati da kamfanoni da ƙungiyoyi.

5. Don siyasa

Kafar sadarwa wata hanyace ta yaɗa manufa da farfaanta da yaɗa manufa da tallata ɗan jam’iyya da jam’iyya don samar da shugabanci na gari ga ‘yan ƙasa da su samu romon dimokuraɗiyya. Don haka, 

Kafafen sadarwa suna taimakawa wajen wayar da kan masu zaɓe da ayyana manufofi da tattaunawar siyasa cikin lumana.Haka wanann kafa tana bayar da bayanan gwamnati. Da tattara ra’ayoyin jama’a.

Fa’idodin kafafen sadarwa:

Sauƙin sadarwa

Mutane suna iya sadarwa cikin daƙiƙu ko da suna ƙasashe daban. Zumunci ya sauƙaƙa rayuwa ta yi sauƙi ta yadda saƙon da za a yi kwanaki kafin ya isa amma ta hanyar wannan kafa a ɗaƙiƙa kaɗan saƙon sai ya isa.  

Samun Bayanai

Ana samun labarai da ilimi cikin gaggawa.

Samar da ayyukan yi da faɗaɗa harkar kasuwanci da samun kwarewa.

Mutane suna samun kuɗi ta hanyar: 

Kirkirar bidiyo.

Rubuce-rubuce.

Tallan dijital.

Koyarwa ta yanar gizo.

Taimakawa Ilimi

ɗalibai da malamai suna musayar ilimi ba tare da iyakacin wuri ba.

Raya al’adu da tallatasu

Ana gabatar da al’adun ƙasa ga duniya.

ƙalubalen amfani da kafafen sadarwa:

Yaɗa labaran ƙarya.

Damfara ta yanar gizo.

Satar bayanan  sirri.

Cin zarafi a yanar gizo.

ɓata lokaci.

Yaɗa maganganun ƙiyayya da ƙarya.

Yaɗa abubuwan da ba su dace ba kamar batsa da tsiraici da sauransu.

Hanyoyin amfani da kafar sadarwa da samar da tsaro:

A yi amfani da kalmar sirri mai ƙarfi.

Kada a bayyana bayanan sirri ga kowa.

A tabbatar da sahihancin labari kafin a tura shi.

A guji buɗe hanyoyin da ba a yarda da su ba.

A danna matakan kariya na asusu (Two-Factor Authentication).

A mutunta dokokin ƙasa da ƙa’idodin amfani da intanet.

Iyaye da malamai suna da rawar da za su taka don inganta kafar sadarwa daga ciki akwai:

Kula da yadda yara ke amfani da kafafen sada zumunta.

Koyar da ɗabi’ar amfani da intanet.

Hana cin zarafi ta yanar gizo.

ƙarfafa amfani da kafafen sadarwa wajen neman ilimi.

Rawar da gwamnati za ta taka

Gwamnati tana da hannu wurin inganta yanar gizo da kai ta matsayi mai girma a cikin al’umma daga ciki akwai:

Inganta hanyoyin sadarwa.

Samar da ilimin fasahar dijital.

Yaƙi da damfara ta yanar gizo.

ƙarfafa dokokin kare bayanan sirri.

Tallafawa bincike da ƙirkire-ƙirkire.

Shawarwari

Duk da wannan fasaha ta bunƙasa  to amma Bahaushe ya ce “in kana da kyau ka ƙara da wanka” to bunƙasar ilimin zai ƙara bunƙasa ilimi da wayewa a cikin al’umma. Yana da kyau a :

A koyar da ilimin amfani da kafafen sadarwa tun daga makaranta.

A riƙa tabbatar da gaskiyar bayanai kafin wallafawa ko turawa.

A yi amfani da kafafen sadarwa wajen bunƙasa ilimi, lafiya, kasuwanci da ci gaban ƙasa.

A guji amfani da su wajen cin zarafi, yaudara ko tayar da fitina.

A ci gaba da koyon sabbin fasahohin dijital.

Kammalawa:

Kafafen sadarwa na zamani sun kawo sauyi sosai a rayuwar ɗan Adam. Sun sauƙaƙa sadarwa, ilimi, kasuwanci da hulɗar jama’a. Duk da haka, amfani da su cikin rashin kulawa na iya haifar da matsaloli masu yawa. Don haka, ya zama wajibi ga kowane mai amfani ya yi amfani da su cikin hikima, gaskiya da bin ƙa’idoji domin amfanin kansa da ci gaban al’umma.

By ukarofi

Leave a Reply