
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar APC ta naɗa Ministan Birnin Tarayya Abuja Nyesom Wike da Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke a matsayin kodinetoci a kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
Wike zai riƙe muƙamin kodineta a Jihar Ribas da Abuja, yayin Adeleke a ɗaya gefen, an naɗa shi a matsayin kodineta a Jihar Osun, a cewar sabon jaddawalin kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar. Waɗannan naɗe-naɗe na zuwa ne gabanin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen, wanda aka tsara yi a ranar Laraba, 14 ga Oktoba, 2026 a babban ɗakin taro na Banquet Hall da ke Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja.
Haka kuma, sabon jaddawalin ya zayyano sunayen Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori a matsayin daraktan kuɗi, yayin da Gwamnan Ogun Dapo Abiodun da Shugaban Hukumar Tattara Haraji ta Ƙasa (NRS), Zacch Adedeji za su zama masu tsara yadda za a tara kuɗi.
Sauran naɗe-naɗen sun haɗa da Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu a matsayin Mataimakin Darakta-Janar na biyu na Shiyyar Kudu da Ministan Ayyuka, David Umahi a matsayin Mataimakin Darakta-Janar na Walwala da Wayar da kai. Sannan, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Ribas Martin Amaewhule shi ne Maitaimakin Kodineta na Kudu maso Kudu don tattar majalisun dokoki.
Shi ma Sanata Ibrahim Ɗankwambo, wanda ɗan jam’iyyar PDP ne ya shiga sahun masu bayar da shawara a kwamitin yaƙin neman zaɓen tare da Obafemi George, wanda zai riƙa bayar da shawara akan harkar yaɗa labarai.
Tawagar yaɗa labaran ta haɗa da Ministan Sufurin Jiragen Sama da Ci-gaban Sararin Samaniya, Festus Keyamo, Abdulmumin Jibrin, Lere Olayinka, wanda mataimaki ne ga Wike da kuma Segun Sowunmi.
Hallau, akwai tsohon Kyaftin ɗin ‘yan wasan Super Eagles, Joseph Yobo a matsayin Mataimakin Darakta ga wayar da kai a fannin wasanni, yayin da ɗan kasuwa Ayiri Emami zai riƙe muƙamin Daraktan Ayyuka na Musamman. Kazalika, tsohon Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje shi ne a matsayin Daraktan wayar da kan masu ruwa da tsaki yayin da tsohon gwamnan Jihar Legas, Babatunde Raji Fashola zai riƙe muƙamin kodinetan tattara masu ruwa da tsaki na Kudu maso Yamma.
Sanata Abdulaziz Yari Yari kuma zai cigaba da kasancewa a muƙaminsa na Darakta-Janar na kwamitin yayin da Sanata Adams Oshiomhole shi ne Mataimakin Darakta-Janar na wayar da kai da Femi Gbajabiamila a matsayin Mataimakin Darakta-Janar na Gudanarwa. Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodimma shi ma zai cigaba da zama a muƙamin Sakataren kwamitin. Sakataren APC Ajibola Bashiru da Hadiza Bala-Usman sune mataimakin sakatare na ɗaya da ta biyu.
Dele Alake ma zai cigaba da kasancewa kakakin kwamitin, yayin da James Faleke zai zama mai sanya ido kan shirye-shiryen zaɓe a matsayin Mataimakin Darakta-Janar. A baya dai, fadar shugaban ƙasa ta kare jaddawalin kwamitin bayan wani cece-kuce akan mutanen da ya ƙunsa, wanda aka fitar a watan Agusta, inda a yanzu ta yi masa kwaskwarima.
