Kano: ‘Yan unguwa sun ƙi karɓar cin hancin N10m don rufa-rufa ga zargin safarar miyagun ƙwayoyi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mazauna Unguwar Bajallabe da ke yankin FCE Gate na 1 a garin Kano, sun ƙi amincewa su karɓi wani tayin cin hanci da aka yi zargin ya kai Naira miliyan 10 domin su yi rufa-rufa ga wata mota da ake zargin ta da jigilar miyagun ƙwayoyi.

Al’amarin ya faru ne a safiyar ranar Talata bayan ‘yan yankin sun gano wata mota ƙirar Golf da ake zargin tana maƙare da haramtattun ƙwayoyi, wadda aka ajiye a gefen wani babur kusa da wani gida da ke unguwar.

Kakakin hukumar jami’an yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Jihar Kano, Lamara Garba ne ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar a ranar Talata. A cewar hukumar, mazaunan sun gano haka ne bayan kusantar motar domin duba abin da yake ciki, matakin da ya sa suka fara zargin samun miyagun ƙwayoyi a ciki.

An zargi direban da yi wa wakilan unguwar da ɗan bijilante tayin Naira miliyan 10 a wani yanayi na ruɗarsu don su kawar da kai daga abin da aka gano. Amma sun ƙi karɓa, wanda a madadin haka suka gayyato hukumomin da suka dace domin su yi bincike a kai.

Jami’an ‘yan sanda da na yaƙi da miyagun ƙwayoyi ne suka halarci wajen, waɗanda suka ce ba a kai ga yanke hukuncin ko miyagun ƙwayoyi ne a ciki ba ko kuma wani abin, inda za a bayyana haka ne yayin da aka kammala bincike.

Shugaban hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyin jihar, Muhyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana matakin ‘yan unguwar a matsayin ƙwarin-gwiwa, sanya ido da ƙoƙarin sauke nauyin zamantakewa, yana mai jinin musu tare da kira a gare su da su ɗore akan haka domin taimaka wa ayyukan fatattakar masu harkar miyagun ƙwayoyi a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

By Babaji

Leave a Reply