Ibrahim Masari hadimin Tinubú da gwamnan Yobe sun bai wa ƙungiyar Izala ta Sheikh Jingir tallafin N600m

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa Ibrahim Masari da gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, sun yi alƙawarin bayar da gudummawar Naira miliyan 600 domin gina Jami’ar Fortune da JIBWIS ke ginawa a Jihar Bauchi.

Masari da Buni za su bayar da Naira miliyan 300 kowannensu.

Sai dai gudummawar ta zo ne a lokacin da ake ta muhawara kan alaƙar siyasa da addini, musamman bayan Shugaban Majalisar Malamai na JIBWIS, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya fito fili yana goyon bayan Shugaba Tinubu da sake zaɓensa a 2027.

Jaridar Daily Trust ta ce an sanar da kyautar ne a yayin wani taro da ƙungiyar ta gudanar a Jos, inda Masari ya sanar da bayar da Naira miliyan 300, yayin da ya ce Gwamna Buni shi ma ya yi alƙawarin bayar da Naira miliyan 300.

Shugaban Majalisar Malamai ta JIBWIS, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya buƙaci Musulmi da sauran masu hannu da shuni su tallafa wa aikin, yana mai cewa jami’ar ba mallakinsa ba ce, kuma idan an kammala ta za ta amfani Musulmi da Kiristoci.

By ukarofi

Leave a Reply