
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar kare ‘yancin kafafen yaɗa labarai (AVRS), ta shiga sahun masana’antar finafinai wajen jimamin rasuwar ɗaya daga cikin mambobinta, jarumi Taiwo Hassan da aka fi sani da Ogogo.
A wata sanarwa da ta fitar ta hannun Shugaban kwamitin yaɗa labaranta, Sani Mu’azu a ranar Talata, AVRS ta ce jarumin ginshiƙi ne daga cikin ginshiƙan masana’antar finafinan Nijeriya kuma jarumin da ƙwarewarsa ta bayar da gagarumar gudunmawa wajen ciyar da harkar gaba a tsawon shekaru da dama.
Ta bayyana cewa, bisa baiwar da yake da ita, ya kasance mai nishaɗantarwa da ilimantar da masu kallo, wanda rashinsa ya haifar da babban giɓi ga harkokin finafinai.
A cewarta, rashin nasa ba iya iyalai ko abokan aiki ya shafa ba, abu ne da ya shafi ilahirin fannin masana’antun nishaɗantarwa.
A ƙarshe, ta yi masa addu’ar Allah ya jiƙan sa ya kuma gafarta masa, tare da bai wa makusantansa haƙurin juriyan rashin sa.
