Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Yayin da ake saura wasu sa’oi a gudanar da bikin ranar Hausa ta duniya ta shekarar 2026, an yi kira ga ɗaukacin al’ummar Hausawa da su fito domin nuna kishin harshensu, tarihinsu da al’adunsu.
Za a gudanar da bikin ne a gobe Laraba, 26 ga Agusta 2026, a fadar Mai Martaba Sarkin Hausawan Najeriya, Amb. Alh. Sani Adamu Geza Garkuwan Hausawan duniya, a Kano.
Shugaban majalisar masarauta ta Arewar mu duniyar mu African Chiefdom and Council, Ambasada Alhaji Ibrahim Haruna, shi ne ya yi kiran, inda ya bayyana bikin a matsayin wata muhimmiyar dama ta haɗa kan Hausawa da kuma ƙara wayar da kan al’umma kan muhimmancin harshen Hausa.
A cewarsa, ranar Hausa ta duniya ba rana ce ta shagali kawai ba, illa wata dama ce ta tunawa da irin rawar da harshen Hausa ya taka wajen haɗa kan al’umma, bunƙasa ilimi da al’adu, da kuma yaɗa tarihin Hausawa a Najeriya, Afirka da sauran sassan duniya.
Ya yi kira ga sarakuna, shugabannin al’umma, malamai, mata da matasa da su halarci taron domin karfafa zumunci da haɗin kai, tare da nuna wa duniya cewa harshen Hausa da al’adunsa suna da muhimmiyar rawa a rayuwar al’ummar Afirka.
Ambasada Haruna ya kuma buƙaci kafafen yaɗa labarai da su ƙara ba da muhimmanci wajen tallata harshen Hausa, tarihin Hausawa da al’adunsu, yana mai gargaɗin cewa gazawar al’umma wajen kare abin da suka gada na iya haifar da ɓacewar wasu muhimman sassa na tarihi.
Ya ce, “abin da ba mu kare ba, tarihi zai iya karɓe shi,” don haka akwai buƙatar Hausawa su haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen kare harshensu da al’adunsu tare da mayar da su abin alfahari ga al’ummomi masu zuwa.
Shugaban majalisar masarautar ya jaddada cewa yana goyon bayan duk wani shiri da zai haɗa kan Hausawa, ya bunkasa harshen Hausa, ya kare al’adunsu tare da samar da kyakkyawar makoma ga matasa.
Ya kuma taya Mai Martaba Sarkin Hausawan Najeriya murna bisa shirya bikin, yana mai addu’ar Allah ya sanya taron ya zama tushen haɗin kai, zaman lafiya da ci gaban Hausawa a Najeriya, Afirka da duniya baki ɗaya.
