2027: Zan cire tallafin fetur, daga bisani na dawo da shi, inji Atiku

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar zai dawo da tallafin fetur idan aka zaɓe shi a 2027, amma daga baya zai cire na wucin-gadi don daidaita lamuran tattali, inji Kakakinsa Paul Ibe.

Ibe ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na AIT, inda ya ce shirin Atiku akan tallafi yana da bambanci da na gwamnatocin baya kuma zai fifita samar da ɗanyen mai da tacewa a cikin gida Nijeriya.

A cewarsa, dawo da shi na wucin-gadi zai bai wa ‘yan Nijeriya da kasuwanci damar numfasawa da farfaɗowa daga matsin tattali da ake fuskanta a yanzu, ƙarfafa harkokin tattalin da ƙara adadin samarwa kafin a sake cire tallafin. Don haka kada a fassara matakin shirin a matsayin dawo da tsohon tsarin tallafi, wanda ya bayyana a matsayin abin da bai bayar da sakamakon da ake buƙata ba ko amfaninsa ya gaza ɗorewa.

A ƙarƙashin shirin nasu, Ibe ya bayyana cewa za a riƙa samar da ɗanyen mai ga matatun gida a farashi mai rahusa da aka sanya wa tallafi, wanda hakan zai bayar da damar samar da fetur da dizal a farashi mai sauƙi.

Wannan, a cewarsa zai taimaka wajen rage tsadar samarwa da kuma samar da sauƙin farashi a gidajen mai ga al’umma, yayin tabbatar da tallafin ya alaƙantu kai-tsaye ga albarkatun ɗanyen man Nijeriya.

Ya ƙara da cewa, za a kafa kwamiti mai zaman kansa da zai riƙa daidaita farashin matata, da kuma duba maslahar yanayin kasuwa.

By Babaji

Leave a Reply