‘Yan bindiga sun ƙone gawar jami’in shige da fice bayan halaka shi a Neja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) reshen Neja, ta tabbatar da mutuwar wani jami’i da ‘yan bindiga suka farmaka yayin wani atisaye a Jihar Neja. Kakakin hukumar, DSI Mukhtar Abubakar ne ya tabbatar da faruwar al’amarin a wata sanarwa da ya fitar a Minna, ranar Litinin.

Abubakar ya ce, an farmaki Mataimakin Sufuritandan Shige da Ficen mai daraja ta I (ASI I), Ibrahim Babagiwa ne tare da wani sufeto a ƙauyen Woko da ke yankin Tungan Waya, a ranar 6 ga Oktoba, a lokacin da jami’an suke gudanar da sintiri a yankin. A yayin harin ne aka halaka Babagiwa, yayin da sufeton ya tsira da raunukan sara, a cewar sanarwar.

Abubakar ya ƙara da cewa, sufeton yana ƙoƙarin farfaɗowa yayin da yake cigaba da karɓar magani. Ya bayyana cewa, an gano gawar Babagiwa ne bayan kwana biyu da aukuwar lamarin, kuma tuni aka masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Kakakin ya jaddada aniyar hukumar ta ƙoƙarin daƙile ayyukan shige da fice ba bisa doka ba da warware sauran matsalolin tsaro a yankunan iyakokin Nijeriya na ƙasa-da-ƙasa.

By Babaji

Leave a Reply