Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce Hausawa na taka muhimmiyar rawa wajen haɗin kai da ci gaban Najeriya, tare da yaba wa gudunmawar da al’ummar ke bayarwa wajen bunƙasa ƙasar.
Tinubu ya bayyana haka ne yayin da yake taya al’ummar Hausawa murnar ranar Hausa, wadda ake gudanarwa a masauratar Daura, da ke jihar Katsina cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.
Shugaba Tinubu ya ƙara da cewa harshen Hausa ya bunƙasa sosai, kuma ya zama wani muhimmin harshen sadarwa da kasuwanci a sassa daban-daban na duniya.
Shugaban ya kuma taya ɗaukacin al’ummar Hausawa murna, yana mai yi musu fatan alheri yayin bikin ranar Hausa ta shekarar 2026.
