
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Dakarun tsaron Shiyya ta 2 na Atisayen FANSAR YAMMA, sun yi nasarar daƙile wani yunƙuri da yin garkuwa da mutane, sannan sun ceto mutum 14 yayin atisayen a Ƙaramar Hukumar Tsafe da ke Jihar Zamfara a ranar Talata.
Wata majiyar tsaro ta shaida wa wakilinmu cewa, an gudanar da atisayen ne a ranar Talata, 25 ga Agusta bayan samun wani bayani na sirri kan lamuran ababen zargi a yankin ƙauyen Magazu.
Akan haka ne rundunar ta tura jami’an tsaro yankin, inda suka yi arangama da maharan da ke ƙoƙarin sace wasu fararen hula ciki har direbobin motoci. A yayin haka ne suka yi musayar wuta a tsakaninsu, wanda hakan ya bai wa sojojin nasara tarw da tilasta wa maharan tserewa da barin abar hawansu yayin gudu zuwa bayan gari.
A lokacin da jami’an suka fara aikin bincike, sun yi nasarar ceto wasu mutane guda 15 aka yi yunƙurin shiga da su daji. Ɗaya daga cikinsu da ya jikkata sakamakon harbin, an garzaya da shi zuwa asibiti domin ba shi kulawa a yankin Tsafe.
Wannan nasara ta nuna yadda ‘yan FANSAR YAMMA suke ƙoƙarin bai wa rayuka da dukiyoyin fararen hula kariya domin hana masu aikata miyagun laifuka sukuni a sassan Jihar Zamfara.
