Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Gidauniyar Sultan watau Sultan Foundation, ta ƙaddamar da wani babban shirin rigakafi a Jihar Zamfara da nufin yiwa yara 80,772 marasa allurar riga-kafi allura a ƙananan hukumomi bakwai waɗanda suka fi samun rashin yiwa yara rigakafi kafin Disamba 2027.
An ƙaddamar da shirin, mai taken Z-TRACE: Bin diddigi a Zamfara da kuma daidaita allurar riga-kafi, a yau Laraba, a wani taron fara aiki na kwana ɗaya da aka gudanar a Karma Guest Inn, Gusau.
Da yake gabatar da jawabin maraba, daraktan shirye-shirye na Gidauniyar Sultan Foundation, Aminu Inuwa Muhammad, ya ce Zamfara tana da kimanin yara 269,241 marasa allurar riga-kafi waɗanda ba su sami allurar riga-kafi ta yau da kullun ba.
Ya lura cewa matsalar tafi ta’azzara a Gusau, Talata Mafara, Shinkafi, Zurmi, Anka, Bakura, da Tsafe.
A cewarsa, an fifita ƙananan hukumomin bakwai ne saboda suna da rashin isasshen tsari, tattara bayanai game da matakin yara, da kuma rashin bin ƙa’ida da suka hana al’umma masu rauni shiga tsarin rigakafin.
Ya ce an zaɓi ƙananan hukumomin Anka, Bakura, Gusau, Shinkafi, Talata Mafara, Tsafe da Zurmi don wannan aikin.
Ya ƙara da cewa dabarun sun yi daidai da muhimman tsare-tsare na Gavi 5.0 da kuma tsarin ci gaban lafiya na ƙasa na Najeriya na III.
Daraktan ya buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki da su goyi bayan aikin, yana mai jaddada cewa nasarar ta dogara ne da ƙoƙarin haɗin gwiwa.
“Waɗannan ba ayyuka ne masu sauƙi ba akwai buƙatar goyon bayan dukkan masu ruwa da tsaki don cimma wannan burin”. Inji shi
Ya buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki da su haɗa hannu don rage yawan yara marasa allurar riga-kafi a faɗin jihar.
Taron ya samu halartar masana, ƙungiyoyin tallafi na ƙasa da ƙasa da sauran masu ruwa da tsaki daga ƙananan hukumomi bakwai da za su amfana da rigakafin.
