Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Hukumar kula da harkokin siyasa ta Jihar Zamfara ta gudanar da taron wayar da kan jama’a na kwanaki biyu da kuma gangamin goyon bayan Gwamna Dauda Lawal da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu a shekarar 2027 a Zamfara.
Bitar ta gudana yau Laraba a Gidan Alh. Umaru Shinkafi, Unguwar Gwaza, kusa da Hedikwatar ‘yan sanda, Gusau.
Da yake jawabi a lokacin taron, mai ba da shawara na musamman ga gwamna kan harkokin Siyasa, Hon. Alhaji Nura Sani Abdullahi, ya ce an tsara wannan gangamin ne don ƙarfafa nasarorin da Gwamna Lawal da gwamnatin Shugaba Tinubu suka samu da kuma samun goyon bayan jama’a gaba ɗaya kafin shekarar 2027.
A cewarsa, ƙungiyoyi 100 na goyon bayan siyasar Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Dauda Lawal a faɗin jihar,tare da da fara aiwatar da gangamin tun kafin babban zaɓen 2027.
Ya yi kira ga mahalarta taron da su yi aiki tare da masu gudanarwa don cimma manufofin ilimin siyasa, daidaita dabaru da kuma ƙarfafa gangamin jama’a a faɗin ƙananan hukumomi 14.
Da yake bayyana taron bitar, Gwamna Dauda Lawal, wanda shugaban ma’aikata, Muktar Lugga, ya wakilta, ya yaba wa ƙungiyoyin 100 kan biyayya da jajircewarsu ga gwamnatin APC.
“Wannan taro shaida ce bayyananna cewa mutanen Zamfara sun yaba da alƙiblar da gwamnatinmu da ta tarayya ke bi a ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Dr. Dauda Lawal.” Gwamna Lawal ya ce.
Gwamna Lawal ya umarci ƙungiyoyin siyasar su 100 da su isar da saƙon nasarorin gwamnati zuwa ga gundumomi da rumfunan zaɓe a matakin jiha da tarayya.
“Yayin da muke tunkarar 2027, dole ne mu kasance cikin haɗin kai, mai da hankali da kuma ladabi. Ku koma ga al’ummominku ku gaya wa mutane abin da wannan gwamnati ta yi da kuma abin da muke niyyar yi.” Inji Gwamna Lawal
