Mataimakin shugabar Tanzaniya ya yi murabus

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Emmanuel Nchimbi, wanda shi ne mataimakin shugabar ƙasar Tanzaniya, ya yi murabus daga muƙaminsa yayin da rikicin siyasa ya yi ƙamari a ƙasar gabashin Afirkan. Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da shari’ar hamɓararwa ta shugaban tsagin adawa, Tundu Lissu.

A ranar Talata, Nchimbi ya miƙa takardar murabus, inda Shugaba Samia Suluhu Hassan ta karɓi matakin nasa, kamar yadda cibiyar yaɗa labaran fadar shugaban ƙasar ta bayyana. A cewar fadar, ajiye aikin nasa zai fara aiki ne a ranar 4 ga watan Satumba, wato wata goma cif kenan bayan kama aiki a ranar 3 ga Nuwamban 2025.

Nchimbi dai ya ce, ya ɗauki matakin ajiye aikin ne domin girmama manufar Shugaba Samia Hassan, yana mai cewa a shirye yake ya haƙura da muƙamin muddin shugabar ta buƙaci wani mataimaki na daban.

Wannan ci-gaba ya biyo bayan zaɓen ƙasar da ya fuskanci cece-kuce ne da aka yi a watan Oktoban 2025, inda aka ayyana Samia a matsayin wadda ta yi nasara bayan samun kaso 98 na adadin ƙuri’un da aka kaɗa.

Bayan zaɓen al’umma sun yi zanga-zanga da kuma janyo suka da zaɓen ya yi daga ƙasashen duniya. Dubunnan mutane aka halaka a sanadiyyar rikicin.

Shugaban CHADEMA Tundu Lissu, wanda shi ne babban abokin hamayyar Samia Hassan, bai samu damar shiga takarar ba kasancewar ana tsare da shi, yayin da aka soke cancantar ɗan takara Luhaga Mpina.

By Babaji

Leave a Reply