Daga RAHMA SABO USMAN
RUBUTAWA: Ayuba Muhammad Danzaki
(ZAKIN MARUBUTA)
SHARHI: Rahma Sabo Usman
SHEKARAR BUGU: 2022
Taƙaitaccen Labarin:
‘Kurman hisabi’ labari ne da aka gina shi a kan jigon ‘Kunnen ƙashi’
Labari ne akan wani kangararren yaro mai suna Umar Niga, yaron da ya yi shuhura gurin tujara da kuma ja wo jarfa. Ya kuma taso a irin yanayin nan da ake kira da albasa da ta ƙi yo halin ruwa, domin kuwa duk inda kake neman mutanen kirki iyayensa sun kai har sun kere.
A kullum rana iyayensa kan zubar da hawayen takaici da baƙinciki ta sanadiyar ɗan nasu. Tujarar tasa ba ta tsaya iya ka nan ba, domin Umar niga ɗan kuka ne mai janyo wa iyayensa jifa. Komai aka yi da sabara sai ta yi kere, wataran a garin tujararsa ya je ya jawo abinda aka naɗa wa mahaifinsa na jaki wanda ya yi sanadin faɗawarsa ga doguwar jiyya ƙarshe ya ce ga garinku nan, bakinsa ɗauke da mugayen kalaman da za su ci gaba da tarwatsa rayuwar Umar. Munafurci shi ya hana a gane mumini, Umar yaɗin mage ne kowa ya tamnaka sai ya yi mai, duk wannan dambarwar da aka yi Nigan gayen ƙemadagas ya busar da zuciyarsa ko leƙe bai ba bare ya ga ko da gawar tsohon nasa. Rabuwa da masoyi ba daɗi, gyatumar Umar ta shiga alhini na rashin mijinta ƙarshe hawan jininta ya tashi ita ma ta ce ga garinku nan.
Tauraruwa mai wutsiya ganinki ba alkhairi a ciki, du mace-macen nan da aka tabka ta sanadiyar niga ba su sanya ya nutsu ba bare ya gane cewar Allah ɗaya ne, sai ma ƙara botsarewa da suka saka shi yi.
Lalatacce lalatacce ne, niga ya tsirfo da mugayen halaye haɗi da ɗora su a kan nashi na da, ƙarshe ya janyo wa kansa jangwam ɗin da zaman Yaryasa ya gagare shi.
Likkafa kuma ta kerewa ta da, daga dirar Umar cikin birnin Kano sai ya shiga aikata ɓarnar da ta kerewa ma kundila, ta hanyar faɗawa manya-manyan harkokin masha’a ciki kuwa har da shiga harkar fashi tare da makami, bayan ya haɗa kai da wasu gaggan abokansa da ya samo a garin Ikko a nan suka tabka ta’asar da sai da ta jijjiga garin Kano.
Likkkafa kuma sai ta ci uban ta da, daga nan fa Umar niga ya zamto sharren tantirin da samun kamarshi sai an tona, da lamari ya yi ƙamari ma sai ya sauya suna daga niga zuwa Faruƙu dala. A irin wannan yanayi na ƙazantacciyar rayuwa ne Umar ya yi aure har ya haihu, lamarin nashi tamkar na makaru ko kuma sanya hannu ganin yana ta ƙara samun bunƙasa ne ya sanya ya cigaba da harkar neman ‘yan kwalta yana kawo su gadon sunna, a nan ne ya haɗu da Binta yarinyar da baƙar tauraruwarta ta cigaba da bibiyar mugunyar rayuwarsa.
‘Yar gagara mai hali irin na kunama, Binta ta samu cikin gaba da fatiha da Umar ƙarshe ya ƙeƙasa ƙasa ya ce bai san zancan ba ya bar ta da kayanta. Bayan ta haihu ta nemi ƙofar wani gida ta yasar da ita ta ƙara lulawa duniya a bar ta.
Barewa ba za ta taɓa gudu ba ɗanta ya gaza rarrafe, ɗan gidan Umar niga shi ya gado mahaifinsa da mummunan halinsa, aminin mahaifinsa kuma wanda ya tsinci ƙanwarsa mai suna Nasiba ya shiga zambata da ci wa amana. Faisal ɗan gidan niga, ya shiga halin tumasanci cikin rufewar ido da ɗiyar mahaifinsa ta ka fi fatiha. Nasiba da Umar li’abbai sun shiga halin bunsuraye da juna, duk da kasantuwar Nasiba matar da ke ɗauke da igiya uku, kuma dukkaninsu na aminin Faisal ɗin wato Najibu.
Idan duniya na yi da kai, ko a kwara ka kasa ruwa sai ka samu masu taya wa. Alhaji Faruƙu dala dukiya ta ƙara bunƙasa ta kuma tunbatsa, inda mai girma gwamna ya nuna shi a matsayin wanda zai gaje shi bayan ya kammala nasa wa’adin, sai dai kuma kifi na ganin mai jar koma talakawa sun yi tutsu sun kuma gano mugun nufin Faruƙu dala, dukda kasantuwar kuɗin da ya narka hakan bai hana sun yi fitar kwarin ɗanga ba sun kuma hane shi da kai wa ga babban mataki.
Duniya budurwar wawa idan ta so sai ta ba ka mota, idan kuma ƙi sai ta kai ka ga mahallaka. Sharri mugun ɗan aike muddin ka saba da aika shi wataran zai dawo maka da aikar da ka yi masa, Faruƙu dala ya gamu da tutsin duniya bayan ta yi mar ƙat ta kuma tona masa asirin da ya jima yana lulluɓewa ta nuna wa duniya waye shi me kuma yake tabkawa a ƙasa. ‘Yan sanda sun yi ram da shi, haɗi da angiza ƙeyarsa shi da abokan ɓarnarsa zuwa gurin manta sabo a nan aka yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Kowa ya bar gida tilashin gida ya bar shi, garin da Umar niga ya yi baƙar rayuwa nan ya yi wasici a mayar da shi bayan an tsayar da haddin Allah a kan shi. Mutanen garin kam sun yi koyi da halayyar manzo ba su duba halin Umar ba suka karɓe shi suka yi masa sutura suka kuma sada shi da makwancinsa na asali. ƙasa ta yi tutsu ta gane Umar ba nata ba ne ta kuma ƙi amsarsa, addu’a da neman gafara a ka duƙufa yi sannan turɓayar ta yarda ta amshi Umar domin ta zamar masa gida.
ƙarshen rayuwar Umar niga, kuma Faruƙu dala.
Yabon Gwani:
Tabbas labarin ya ginu ta hanyar ba shi salo mai armashi da kuma tsuma zukatan makaranta. Labarin ya ƙayatu ainun ta hanyar fito da lalatattun yaran da ke koyon mugayen ɗabi’u tun daga haihuwa. Marubucin ya fito da abinda ke damun rayuwakanmu, musamman a kan ‘yan siyasar yanzun da ke handame dukiyar al’umma su aikata maƙociyar ƙasa ko kuma nesa da ƙasar gabaɗaya, ‘yan siyasar ba su tsaya nan ba sukan ɗebi bara-gurbi daga mutanen da suka aminta da su, suka kuma yarda da cewar za su bar su su cigaba da sharholiyarsu ko da kuwa kujera ta bar hannayensu.
Marubucin ya fito da al’adar wasu mutanen ta saurin amincewa da mutane, kamar yadda nagartaccen mutum Alhaji Yusuf nadabo ɗan aljanna, ya aminta da makirin mutum irin niga ya janyo shi jikinsa ƙarshe ya zame masa ɗan agwagwa. Haka ma kuma Alhaji Yusuf ɗin ya nuna halin dattaku ta hanyar ƙin yarda da maganar tsintacciyar mage, inda ya aurawa tilon ɗansa yarinya da ya tsinta a kwararo daga ƙarshe ta ƙarasa masa karin maganar na cewa ba ta mage.
Marubucin ya yi matuƙar ƙoƙari gurin haskawa mutane yadda tarbiya ta lalace, rayuwa kuma ta zamto abar tsoron da ba a aminta da kowa. Domin kuwa amini zai iya cin amanar amini ko a kan gadon kwanansa ne.
Kurakurai:
Duk cikar ɗari ba ta kai ga dubu ba, duk kyawun abu ba ya rasa kushe. Marubucin littafin ya ɗan kuskuro ta waɗansu abubuwa ƙalilan.
Da fari ya nuna mahaifin Umar mutum ne mai ƙana’a, haɗi da tsoron Rabbissamawati amma daga ƙarshe laifin da ba nashi ba sai da ya shafe shi, alhalin ko Allah Ba ya hukunta wani da mugun nufin wani.
Duk wannan ta’asa da sharholiyar da niga yake, ko sau ɗaya bai taɓa shiga komar hukuma ba ba kuma ya taɓa yin rayuwa a jarum ba anya kuwa a rayuwa ta zahiri ana samun haka? Na rasa gane ta yaya karan tabar da ba a kunna ba, ya yi sanadiyar tayar da gobara? Umar ya ji sanarwa a radiyo cewar ana neman sa shi da wasu masu mugun nufi irin sa, ƙarshe ya tarkata kadarorinsa ya ci layar ɓata, bayan zakara ya ba shi sa’a ya ari na kare zuwa ga wata duniyar. Tambayata a nan anya kuwa ɗansanda zai yarda ya yi holon sunan babban mai laifi ba tare da ya damƙi ɗamarar zuwar masa ta duk inda ya ɓullo ba?
ɗan takarar gwamna a babbar jiha, a ce har ya gama takararsa ba a gano yana cikin wanda hukuma take nema ruwa a cikin jallo ba? ‘Yan garin yaryasa sun kasa gane cewar Umaru niga nasu ne, duk kuwa da shuhura da ya yi a kafafen sadarwa, a kuma ce ‘yan jam’iyar adawa sun kasa zuwa su binkito wa duniya laujen da ke naɗe? Ko kuma su ‘yan garin sun kasa gane shi a fosta, sun kuma gaza gano shi ya yin da yake rattaba jawabi a gidan radiyo? Haba wannan ma da sake. Bai kamata a ce duk tsiyar da Umar ya shuka, an samu masu koka masa bayan ya mutu ba, garin banza a faraufarau ɗin banza ya kamata ya ƙare Nasiba da Faisal kamata ya yi a ce sun ƙyamace shi har bayan mutuwarsa. Zancan ƙasa ta kasa ɗaukar mutum anya kuwa ba tatsuniya ba ce ko kuma shifcin gizo ba? Bai zo a nassi ba cewar ƙasa za ta kasa ɗaukar mujiri ba, duk kuwa da yadda ya kai ga iya tabka mujirimancinsa, tunda ai ba zai ka ya Abu lahabi; ƙaruna; Bin Salul da dai sauran su ba. Amma kuma duk ba mu ji tarihin cewar ƙasa ta yi tsutsu ya yin da aka jefa su cikinta ba.
Kammalawa:
Ina roƙon Allah Ya ƙara wa marubucin fikra haɗi da tarin baiwa da fasaharsa cigaba da ƙirƙiro daɗanɗan rubutu waɗanda za su nishaɗantar su kuma faɗakar.
