An halaka sanannen jagoran ‘yan bindiga, Sani Yello a Zamfara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewa an halaka fitaccen shugaban ‘yan bindiga Kachalla Sani Yellow a Ƙaramar Hukumar Anka, wanda ya shahara wajen jagorantar hare-hare, garkuwa da mutane da satar shanu a Jihar Zamfara da wasu sassan Arewa ta Yammacin Nijeriya.

Saidai rahotanni sun bambanta kan yadda aka halaka shi, inda wasu majiyoyi suka ce an harbe shi ne a kasuwar Dan Jibga da ke ƙaramar hukumar yayin da ake zargin mabiyan jagoran ‘yan bindiga Dogo Gide ne suka farmake shi.

Wani rahoton kuma ya ce, an ya nasarar halaka shi ne a wani samamen haɗin-gwiwa da jami’an tsaro da ƙungiyar Maiduguri Special Vigilantes suka ƙaddamar.

Haka kuma, an kuma ruwaito cewa wasu ‘yan bindiga da ake zargin mabiyan Adamu Aliero ne suka kai sabbin hare-hare a ƙaramar hukumar Tsafe, inda aka halaka mutune biyu tare da yin garkuwa da sama da mutane 60 jim-kaɗan bayan faruwar al’amarin.

Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da sanarwa ta musamman ba akan yadda al’amarin ya kasance.

By Babaji