Kofin Duniya: Ingila za ta kara da Argentina a wasa dab da na ƙarshe bayan doke Norway

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An tabbatar da wasannin zagayen dab da na ƙarshe na gasar Kofin Duniya ta 2026, inda manyan ƙasashe huɗu suka tsallake zuwa wannan mataki bayan fafatawar da suka yi a zagayen wasannin dab da na kusa da na ƙarshe.

Ingila za ta fafata ne da Argentina ranar 15 ga Yuli, 2026. Hakan na zuwa ne bayan doke Norway da ci 2 da 1 yayin da wasan ya kai zangon ƙarin lokaci.

Ita ma Argentina ta yi nasarar kaiwa zagayen ne bayan doke Switzerland ta su Granit Xhaka da ci 3 da 1 su ma a zangon ƙarin lokaci.

Mac Allister, Julian Alvarez da Lautaro Martinez ne suka zura ƙwallayen da Argentina ta ci yayin da Messi ya bayar da ɗaya daga ciki.

A ɓangare na biyu kuwa, Faransa za ta kara da Sifaniya ranar 14 ga Yuli, 2026. Hakan na zuwa ne bayan da ƙasashen suka tsallake zuwa zagayen sakamakon nasarorin da suka yi a baya.

Masoya ƙwallon ƙafa a faɗin duniya na cigaba da ɗokin kallon waɗannan manyan wasanni, waɗanda ake sa ran za su kasance cikin mafi kayatarwa a gasar.

By Babaji