Kotu ta umarci ‘yan sanda su girke lauya a kowane ofishin rundunar a Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kotin Masana’antu ta Ƙasa a Abuja, ta umarci Rundunar ‘Yan sandan Nijeriya da ta girke lauya guda a kowane ofishinta da ke sassan ƙasar bisa la’akari da hukuncin kundin dokokin ‘Yan sanda na 2020.

Mai Shari’a O.Y Anuwe ne ya bayar da umarnin a ranar Juma’a yayin hukunci akan ƙorafin da kwamitin amintattun Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA) ya yi akan Hukumar kula da lamuran ‘Yan sanda (PSC) da wasu ɓangarori biyar.

Haka kuma, kotun ta haramta wa jami’an ‘yan sanda da ba mambobin tawagar shari’a ba su riƙa wakiltar rundunar a shari’un fararen hula.

Mai shari’ar ya kuma yi watsi da ƙorafin PSC na ƙalubalantar ƙara da matsayar NBA na ɗaukar matakin, musamman wajen neman kotun ta yi ƙarin haske akan naɗi ko ayyukan da suka shafi ‘yan sanda lauyoyi.

NBA a ƙarar ta ce gama-garin ‘yan sanda da dama suna aiki a matsayin ‘yan sanda lauyoyi ba tare da cancanta ko ƙwarewa ba kamar yadda shari’a ta tana.

A cewar alƙalin, ƙungiyar tana da damar shigar da ƙara bisa la’akari da hukuncin doka akan al’amarin da kuma bayar da kariya ga harkar shari’a da tabbatar da biyayya ga dokokinta.

By Babaji