Shugaban ƙasar Guinea ya sallami sojoji 173

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Janar Mamadi Doumbouya na Guinea, ya sallami dakarun sojin ƙasar guda 173 daga aiki bisa zargin barin wajen ayyukansu ba tare da izini ba.

Gidan talabijin na ƙasar ne ya sanar da matakin a ranar Litinin, 24 ga Agusta, 2026. Janar Amara Camara, wato Sakataren gwamnatin mulkin sojin ƙasar ne ya sanar da matakin a madadin fadar Shugaban ƙasar.

Daga cikin waɗanda matakin ya shafa akwai Kwamanda Michel Lamah, wanda ya kasance ɗaya daga cikin manyan jami’an rundunar Forces Spéciales, kuma ya taka rawa a juyin mulkin da ya hamɓarar da tsohon Shugaba, Alpha Condé a ranar 5 ga Satumban 2021.

Matakin na zuwa ne yayin da gwamnatin Doumbouya ke ƙoƙarin ƙara ƙarfafa ladabtarwa, biyayya da inganta rundunar sojin ƙasar.

Haka kuma, matakin ya sake janyo hankalin jama’a akan sauye-sauyen da ake samu a cikin rundunar sojin Guinea tun bayan juyin mulkin 2021.

By Babaji

Leave a Reply