
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hedimastan makarantar Nomadic Basic School da ke Igbojaye a Ƙaramar Hukumar Itesiwaju ta Jihar Oyo, Mista Mathew Kolawale Owoade ya shaƙi iskar ‘yan bayan garkuwa da shi da aka yi na tsawon kusan sa’o’i 48.
An sako hedimastan mai shekaru 60 ne da misalin ƙarfe 6 na yammacin ranar Litinin, 13 ga Yuli, 2026.
Da fari, masu garkuwar sun buƙaci a biya Naira miliyan 30 a matsayin kuɗin fansa, inda iyalan suka yi magiya akan su karɓi miliyan N3, wanda da farko sun amince.
Bayan iyalan sun tara miliyan N3, an yi zargin cewa ‘yan bindigar sun ƙara kuɗin zuwa miliyan N5.
Haka kuma, an ruwaito cewa sai da iyalan suka biya miliyan 5 kafin aka sako Mista Owoade a kusa da ƙauyen Ajebamidele, inda bayan haka ne ya koma cikin iyalan nasa.
Da take tabbatar da al’amarin, Rundunar ‘yan sandan Oyo, ta ce an sace dattijon ne akan hanyar dajin yankin Igbojaye zuwa Budo Aare a ranar 12 ga Yuli, 2026.
Akan haka ne kakakin rundunar, Ayanlade Olayinka ya ce aka gaggauta tura jami’an tsaro domin gudanar bincike akan al’amarin.
A cewarsa, matsi na jami’an hukumomin tsaro ne ya tilasta wa ‘yan bindigar sako shi a yammacin na Litinin, yana mai cewa an garzaya da shi asibiti domin duba lafiyarsa.
