Tinubu ya umarci NIMC ta yi wa dukkan ‘yan Nijeriya rajista nan da ƙarshen 2026

Spread the love

A ranar Litinin Shugaba Bola Tinubu ya umarci Hukumar Kula da lamuran Shaidar Ƙasa ta (NIMC) da ta tabbatar an yi wa baki ɗaya ’yan Nijeriya rajistar shaidar zama ɗan ƙasa kafin ƙarshen shekarar 2026.

Wannan umarni ɗaya ne daga cikin ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na gina cikakken tsarin tantance ’yan ƙasa domin inganta gudanar da mulki, tsare-tsaren gwamnati, da kuma sauƙaƙa isar da ayyuka da tallafin gwamnati ga al’umma.

Ana sa ran wannan shiri zai taimaka wajen samar da ingantaccen bayanan ’yan ƙasa, ƙarfafa tsaro, bunƙasa tattalin arziki, da kuma tabbatar da cewa kowane ɗan Najeriya yana da cikakkiyar shaidar zama ɗan ƙasa.

Gwamnatin ta kuma jaddada cewa kammala rajistar shaidar ƙasa ga dukkan ’yan Nijeriya zai kasance wani muhimmin mataki wajen inganta tsarin gudanar da gwamnati da kuma samar da ingantattun ayyuka ga jama’a a ƙasar.

By Babaji

Leave a Reply