Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Ba da jimawa ba ne aka gudanar da wani taron matasa ’yan Arewa masu rubuce-rubuce a zaurukan sada zumunta, a wani yunƙuri na haɗa kan matasan maza da mata, ƙarfafa musu gwiwa, da kuma samar musu da wata alƙibla ta yadda rubuce-rubucen da suke yi za su riƙa samar musu da natija mai kyau.
Ofishin babban mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin watsa labarai da wayar da kai, Abdul’Aziz Abdul’Aziz ne ya shirya wannan taro, wanda aka gudanar a babban ɗakin taro na fadar gwamnatin Kano, a ranar Litinin 6 ga watan Yuli, 2026. Kuma taron ya yi ƙoƙari wajen gayyato fitattun marubuta, ’yan jarida, da ’yan siyasa, da suke da ruwa da tsaki kan harkokin wayar da kan jama’a da rubuce-rubuce a zaurukan sada zumunta da jihohin Arewa daban-daban.
Kodayake ban samu damar halarta ba, ba kuma don ba a tura min da gayyata ta musamman ba, sai dai wasu harkoki na aiki da suka sha ƙarfina. Amma babu shakka naso kasancewa a taron saboda wasu dalilai. Daga ciki akwai batun kasancewata ɗan jarida daga Arewa, inda nan ne mazaɓata, kuma inda na fi sani nake kuma ba da gudummawata. Sannan ina daga cikin jagororin ƙungiyar Marubutan Arewa a soshiyal midiya, wacce ke ƙarƙashin jagorancin Haidar Hasheem Kano, wato Arewa Media Writers, ƙungiyar dake kan gaba wajen ilimantar da matasa marubuta a zaurukan sada zumunta, da kuma wayar da kan ’yan Arewa kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi cigabansu da rayuwarsu. Kodayake wannan ba taron mu ba ne, kuma babu haɗin gwiwa a tsakanin ɓangarorin biyu. Sannan harwayau wanda yake jagorantar taron Abdul’Aziz Abdul’Aziz abokin aikina ne, wanda nake matuƙar ganin kimarsa da mutuncin sa, don haka ina kyautata zaton fitowar wannan taro daga ofishin sa abu ne da zai haifar da alheri ga ’yan gwagwarmaya na Arewa.
Sai dai duk da kasancewar ban samu halarta ba, na bibiyi yadda taron ya kasance, da abubuwan da aka tattauna akai. Har ma da ra’ayoyin da jama’a da suka riƙa fitarwa bayan taron wanda yake bayyana tasirin taron ko akasin hakan. Mafi akasarin abubuwan da na ga jama’a na kuka a kai, shi ne yadda taron da ake tunanin an yi shi ne don haɗa kan marubutan Arewa da samar musu da alƙibla kan yadda za su tunkari ƙalubalen dake fuskantar yankin a rubuce-rubucen su, sai kuma aka ga ba haka abin yake ba. Wasu na ganin an karkatar da taron zuwa na siyasa domin taya shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf yaƙin neman zaɓe.
Sannan hatta mutanen da aka gayyata zuwa taron akasari magoya bayan jam’iyya mai mulki ta APC ne, ko kuma ’yan jagaliyar siyasa a soshiyal midiya, waɗanda aikinsu bai wuce na ‘Data Boys’ ba. To, ko ma dai mene ne gaskiyar waɗannan zarge-zarge, abin da ya fito fili shi ne an yi taro cikin tsari da lumana, kuma ya yi tasiri, don haka ne ma ake ta kwakwazon magana a kai. Kodayake kowanne abu irin wannan ba zai rasa ƙalubale ba, kuma ya kamata waɗanda suka shirya taron su kare su da buɗaɗɗiyar zuciya ba tare da shigar bambancin ra’ayi ko siyasa a ciki ba, saboda nan gaba a yi gyare-gyaren da suka kamata.
Na ji daɗin bayanan da aka rawaito cewa Ministan Watsa Labarai Muhammad Idris da shi uban gayya Abdul’Aziz Abdul’Aziz sun bayyana, game da kira da marubuta ba soshiyal midiya su kaucewa yaɗa farfagandar ’yan ta’adda a shafukansu, da kuma taimakawa wajen wayar da kai ga jama’a game da ƙoƙarin da gwamnati da jami’an tsaro ke yi na inganta tsaro, ƙoƙarin alƙawuran da aka yi wa jama’a lokacin yaƙin neman zaɓe, da sauransu.
Lallai waɗannan saƙonni ne masu muhimmanci da ya kamata masu riƙe da waɗannan ofisoshi su mayar da hankali a kansu, kuma cigaba da ambatonsu a ko’ina, har sai jama’a sun fahimce su. Duk kuwa da kasancewar ba zai hana manazarta da ýan adawa zargin akwai siyasa a ciki ba. Lallai matasan Arewa na buƙatar jagoranci da tarbiyya, yadda za su fitar da baiwar da suke da ita ga cigaban rayuwar su da ta al’ummar su.
Nima daga gefe guda ina son in yaba wa Babban Mai Bai Wa Shugaban ƙasa Shawara Kan Harkokin Watsa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Abdul’Aziz Abdul’Aziz, bisa tunanin shirya wannan taro, wanda an jima da buƙatar ganin an samu hakan. Ya kamata in da hali a cigaba da shirya irin hakan lokaci zuwa lokaci, a riƙa samar da jigon da za a tattauna a kai wanda ya shafi al’ummar Arewa da ƙalubalen ta, tare da gabatar da maƙalu ko bincike da za a gabatar wa gwamnati, don a yi aiki da shawarwarin da aka gabatar. Wannan zai taimaka sosai, ba kawai ga matasa marubuta ba, har ma da yankin Arewa da kuma uwa-uba gwamnati da kanta.
Sannan yana da muhimmanci a ga an kawar da duk wani abu da zai ba da ƙofar zargin hannun gwamnati ce ta ɗauki nauyi ko kuma siyasa ake so a yi. Kamar wannan kashin farko da aka yi shi a ɗakin taron fadar gwamnati, wannan kuskure ne, in da so samu ne a samu wani waje da zai zama tsakatsaki, bai shafi kowanne ɓangare ba. Harwayau, a sanin mu, idan aka ce Arewa ba yana nufin Musulmi kaɗai ba, yana magana ne jan dukkan al’ummar Arewa, Hausawa, Fulani, Kanuri, Nufawa, Katafawa, Jarawa, Gwarawa, Arago, Tubawa, Berom, Margi, da duk sauran ƙabilun Arewa, manya da ƙanana, Musulmi da Kirista. Ya kamata a samar da wakilci na dukka manyan addinanmu, ba tare da nuna fifiko ba.
Yana da muhimmanci a haɗa gwiwa da sauran manyan ƙungiyoyin matasa na Arewa, ’yan gwagwarmayar samar da cigaba, ’yan ƙwadago, da masu kare haƙƙoƙin ɗan adam. Kar a manta da mutane masu buƙata ta musamman, da tsiraru masu gwagwarmayar a saurari buƙatunsu a hukumance. A yi ƙoƙari a ga ba a sauka daga kan manufar da ta sa aka ɓullo da taron ba. Dama kuma babu wani abu da mutum zai ɓullo da shi ba tare da ya fuskanci adawa ko ƙalubale ba, amma jajircewa da tsayawa kan manufa, ita ce za ta sa har wanda ba ya tare da tafiyar shi ma ya shigo a yi tare da shi.
Da fatan nan gaba idan za a kira wani taron a riƙa kewayawa da shi zuwa wasu jihohin Arewa, don kowacce jiha ta ba da tata gudunmawa, kuma a bai wa kowa zarafin shiga a yi da shi. A yi ƙoƙarin ganin tafiyar ba ta watse ba, kamar yadda a bata muka ga ire-iren waɗannan manufofi sun ɓullo, jama’a sun karɓa, daga baya kuma gayyar ta watse.
Allah Ya haɗa kan matasan Arewa, Ya yi mana jagoranci ga yin abin da yake daidai, don cigaban Arewa da Nijeriya bakiɗaya.
