‘Yan ta’adda sun kashe jami’an tsaron daji biyu a Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Rahotanni daga ƙaramar hukumar Danko-Wasagu sun bayyana cewa aƙalla jami’an tsaron daji (Forest Guard) biyu sun rasa rayukan su bayan bata-kashi tsakanin su da waɗansu mahara
da a ke sa ran masu garkuwa da mutane ne da suka kai farmaki a gonakin garin Tudunbichi a garin Wasagu safiyar litinin.
Wani mazaunin garin na Wasagu da bai so a bayyana sunan sa ba saboda dalilan tsaro ya bayyana cewa da rana ne maharan suka kai farmakin, bayan sanar da jami’an su kuma cikin lokaci suka kai wa mutanen garin ɗauki inda a ka yi musayar wuta na wani lokaci.

Ya ƙara da cewa an samu rashin sa’ar rasa wasu daga cikin jami’an tsaron Forest Guard guda biyu da suka haɗa da Mansir Sani Binoni da kuma Nasiru Dodo Tudunbichi.
Ya ce maharan sun gudu duk da ya ke da yawa daga cikin su sun sami raunuka daban-daban amma dai ƴan uwan su sun gudu da su.

Wannan yankin a halin yanzu dai nan ne mahara ke cin karen su ba babbaka saboda a kullum sai an kai hari a ƙauyukan da ke wannan yankin ko cikin dare ko kuma da safe.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton babu wata sanarwa daga ƙaramar hukumar mulki ta Danko-Wasagu ko kuma hukumomin tsaro.

By ukarofi

Leave a Reply