Tashar lantarki ta Lambar Rimi: Daga shekarun tsaiko zuwa hanyar kammala aiki a bayyane

Spread the love

Daga ABUBAKAR TUKUR IBRAHIM

Korafe-ƙorafen da ake yi dangane da tashar samar da wutar Iska ta Lambar Rimi abu ne da ya dace.

Kowanne ɗan jihar Katsina na son ganin injinan samar da wutar suna aiki tare da ganin an fara isar da wutar lantarki zuwa gidaje, wuraren kasuwanci, masana’antu da al’ummomi. Sai dai kuma, duk da cewa yana da sauƙi a yi bayanin tarihin aikin, yana da muhimmanci a bayyana gaskiyar abubuwan da suka faru a ƙarƙashin jagorancin mai girma Gwamna Malam Dikko Umaru Raɗɗa, PhD, CON, wajen ceto aikin daga shekaru masu yawa na rashin tabbas tare da sanya shi kan turbar kammalawa.

Lokacin da Gwamna Raɗɗa ya karɓi ragamar mulki a shekarar 2023, ya tarar da wani aiki da ya zama alamar damar ci gaba da ba a cimma ba. Tashar samar da wutar ba mallakin Gwamnatin Jihar Katsina ba ce, kuma ba ta ƙarƙashin ikon gwamnatin jihar take ba. Ta kasance kadara ce ta Gwamnatin Tarayya wadda ta fuskanci matsaloli na lalacewar fasaha, ɓarna, rashin kammala gwaje-gwajen ƙarshe, rashin tabbas kan mallaka da kuma rashin tsarin gudanarwa mai ɗorewa.

Mutane da dama kafin shi sun yi magana kan aikin. Amma Gwamna Raɗɗa ya zaɓi ɗaukar mataki.

Da yake fahimtar muhimmancin aikin ga makomar Jihar Katsina, mai girma gwamnan ya bayar da umarnin samar da cikakken tsarin tattaunawa da masu ruwa da tsaki. Hakan ya haifar da tattaunawa mai zurfi da ma’aikatar wutar lantarki ta tarayya, hukumar kula da kasuwancin kadarorin gwamnati (BPE), hukumar kula da yarjejeniyar zuba jari ta ababen more rayuwa (ICRC), kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano (KEDCO), da kuma kamfanin ƙera kayan aikin na asali, wato Vergnet na ƙasar Faransa.

A wata alama ta shugabanci na gari da jajircewa, Gwamna Raɗɗa ya kai ziyara da kansa zuwa ƙasar Faransa domin ganawa da kamfanin Vergnet. Maimakon dogaro kawai da rahotanni da bayanai, ya ziyarci masana’antar kamfanin, ya duba fasahar da ake amfani da ita da kansa, ya tattauna da ƙwararrun masana tare da neman hanyoyin da suka dace domin gyara da kammala aikin.

Wannan ba ziyara ce ta al’ada ko ta nuna kai ba. Ziyarar aiki ce domin farfaɗo da wani aiki da ya kwanta tsawon shekaru.

Sakamakon wannan tattaunawa kai tsaye, an gayyaci kamfanin Vergnet domin gudanar da cikakken binciken fasaha a tashar. Binciken ya tantance duka injina 37 na samar da wutar, ya gano irin lalacewar da kowanne ya samu, ya ware irin gyaran da ake buƙata tare da ƙididdige kuɗin gyaran da kuma hanyoyin aiwatar da su domin mayar da tashar zuwa cikakken aiki.

Baya ga wannan aikin fasaha, gwamnatin ta ɗauki wani mataki da babu wata gwamnati da ta gabata da ta samu nasarar yi, wato shirya da gabatar da takardar tsarin kasuwanci (Outline Business Case – OBC) ga hukumar ICRC domin miƙa aikin, kammala shi da kuma kasuwantar da shi.

Inganci da ƙwarewar wannan takarda sun samu kyakkyawar amincewa daga ma’aikatar wutar lantarki ta tarayya, ICRC da BPE. Sakamakon haka, kwamitin haɗin gwiwa na waɗannan hukumomi ya ba da shawarar a miƙa tashar samar da ƙutar iska ta Lambar Rimi ga Gwamnatin Jihar Katsina, bisa la’akari da ƙwarin gwiwa, shirin aiki da jajircewar jihar wajen kammala aikin. Wannan babban ci gaba ne da ba za a iya yin watsi da shi ba.

Gwamna Raɗɗa ya fahimci cewa gyara tashar kaɗai bai isa ba. Tsarin makamashi na duniya ya sauya, kuma ɗorewar samar da makamashi yanzu na buƙatar hanyoyi daban-daban na samar da wuta. Saboda haka, gwamnatin ta ƙara tsara yadda za a haɗa tashar da tsarin samar da wutar hasken rana mai yawa tare da na’urorin adana makamashi na batir.

Manufar a bayyane take: mayar da Lambar Rimi daga tashar samar da wutar iska kaɗai zuwa cibiyar samar da makamashi mai sabuntawa ta zamani, wadda za ta samar wa al’ummar Katsina wutar lantarki mai inganci, mai ɗorewa da araha.

Har ila yau, yana da muhimmanci a bayyana cewa gwamnatin ba ta taƙaita manufofinta na makamashi ga tashar Lambar Rimi kaɗai ba. A ƙarƙashin jagorancin Gwamna Raɗɗa, Jihar Katsina ta samar da cikakkiyar manufar makamashi, ta shirya tsarin haɗaɗɗen albarkatun makamashi tare da haɗin gwiwar ƙasashen waje, ta samar da ƙananan tashoshin hasken rana da tsarin hasken rana masu zaman kansu a asibitoci, makarantu, cibiyoyin gwamnati da al’ummomi.

Haka kuma, gwamnatin ta amince da samar da megawatt 20.1 na hasken rana a muhimman cibiyoyi, ta fara shirye-shiryen motocin lantarki, ta faɗaɗa aikin samar da wutar lantarki a karkara tare da haɗin gwiwa da masu zuba jari a fannonin samar da wutar ruwa, gas da makamashi mai sabuntawa.

Waɗannan ba alƙawura ba ne. Ayyuka ne da ake iya aunawa. Masu neman jadawalin lokacin kammala aikin sun cancanci a yi musu bayani dalla-dalla. Amma shugabanci na gari na buƙatar a gina jadawalin lokaci bisa haƙiƙanin yanayin fasaha, amincewar hukumomi, tsare-tsaren samar da kuɗi da kuma hanyoyin miƙa mallaka, maimakon yin furucin siyasa domin jawo hankalin jama’a.

Abin da ya kamata al’ummar Katsina su sani shi ne cewa: a karon farko tun bayan fara wannan aiki, akwai cikakken binciken fasaha, shirin gyara a sarari, goyon bayan hukumomi wajen miƙa aikin, tsarin kasuwantarwa da kuma hanyar haɗa tashar da wasu hanyoyin samar da makamashi.

Wannan bai faru da kansa ba. Ya faru ne saboda Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ya ɗauki matakin cewa tashar Lambar Rimi ba za ta ci gaba da kasancewa abin tunawa na damar da aka rasa ba.

Gwamnatinsa na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da cewa tashar samar da wutar iska ta Lambar Rimi ta fara aiki tare da zama ginshiƙi wajen bunƙasa masana’antu, samar da wadatacciyar makamashi, haɓaka tattalin arziki da samar da ayyukan yi a Jihar Katsina.

Al’ummar Katsina suna da haƙƙin neman sakamako. Gwamna Radda ma ya amince da hakan. Wannan ne ya sa ya fi mayar da hankali wajen warware matsalar maimakon ci gaba da tattaunawa a kanta. Tafiyar ba ta kai ƙarshe ba tukuna, amma a karon farko cikin shekaru masu yawa, an fara ganin ƙarshen tafiyar a sarari.

Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa bai gaji matsalar ba, amma ya karɓi alhakin warware ta. Wannan shi ne shugabanci. Wannan shi ne jajircewa. Kuma wannan shi ne bambancin da al’ummar Katsina suka fara gani.

Malam Abubakar Ibrahim wani ɗan ƙasa ne mai kishin ci gaban jihar Katsina

By ukarofi

Leave a Reply