
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An dakatar da sauraron ƙarar da aka shigar akan Darakta Janar na hukumar bogi ta PFIPC, Adeniyi Adeyemi sakamakon rashin bayyanarsa a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Talata.
Ana sa ran ganin Adeyemi ya bayyana a gaban Alƙali Mohammed Umar ne kan tuhume-tuhume guda takwas da suka shafi zarge-zargen bogi, damfara da sojan gona da aka shirya gabatarwa akansa.
Ana ganin Sufeto Janar na Rundunar ‘Yan sanda da ya shigar da ƙarar akan Adeyemi, ya nemi kotun ta bayar da izini domin kamo shi a duk inda yake.
A ranar 27 ga Nuwamban 2025 ne aka maka Adeyemi da wasu mutane biyu a kotu daga ɓangaren lauyan ‘yan sanda, Wisdom Madaki.
Daga cikin shaidun da aka zayyano domin su tabbatar da al’amarin, akwai Shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, Paul Emmanuel, Jeremiah Imoukhede da kuma Ituah Sylvester.
Adeyemi, wanda har zuwa ranar Litinin ba a san inda yake ba, ya bayyana cewa ya janye shiga hada-hadar al’umma ne kan barazanar halaka shi da ya yi iƙirarin ana yi.
Ya kuma yi watsi da batun cewa yana guje wa kamen hukumomin tsaro ne ko yunƙurin ƙaddamar da bincike akansa kan zargin badaƙalar hukumar bogin.
