Daga ABUBAKAR A. BOLARI Gombe
Ƙungiyar dangin juna Afirka Initiative (DJAI) ta karrama babban mataimaki na musamman ga Gwamnan Jihar Gombe kan harkokin tsaro da hulɗa da sauran hukumomi, Ambasada Yusuf Musa Danbayo, da lambobin yabo guda biyu saboda ayyukansa na jin ƙai da gudummawar da yake bayarwa wajen ci gaban al’umma.
An miƙa lambobin yabon ne a wajen bikin rufe taron ƙasa na DJAI na National Retreat 0.2, wanda aka gudanar a Yankari Game Reserve da ke Jihar Bauchi.
Da yake gabatar da lambobin yabon, shugaban ƙungiyar na ƙasa, Usman BK, ya ce an zaɓi Danbayo ne saboda jajircewarsa wajen gudanar da ayyukan jin ƙai da ci gaban al’umma ta hannun ƙungiyoyin AC4D da Gidan Alheri.
Ya bayyana cewa gudummawar Danbayo wajen ƙarfafa matasa, haɓaka aikin sa-kai da tallafa wa marasa galihu ta yi tasiri mai kyau ga rayuwar mutane da dama tare da zaburar da wasu su rungumi hidimar al’umma ba tare da son kai ba.
Usman ya kuma yi kira ga mambobin ƙungiyar da su yi koyi da Danbayo ta hanyar ci gaba da sadaukar da kansu ga ayyukan jinƙai da shirye-shiryen da ke inganta ci gaba mai ɗorewa a cikin al’umma.
A nasa jawabin bayan karɓar lambobin yabon, Danbayo ya gode wa shugabannin DJAI na ƙasa, mambobin ƙungiyar da kuma reshen Gombe na Gidan Alheri bisa ganin ya cancanci wannan karramawa.
Ya bayyana cewa lambobin yabon ba wai girmamawa kawai ba ne, har ila yau ƙalubale ne da ke ƙara masa ƙwarin gwiwar ci gaba da hidimtawa al’umma.
Ya ce, “Ina matuƙar farin ciki tare da godiya bisa wannan karramawa ta lambobin yabo guda biyu da aka ba ni a ƙarshen taron ƙasa na DJAI retreat 0.2 saboda jajircewata wajen ayyukan jinƙai ta hannun AC4D da gidan alheri.”
Danbayo ya ƙara da cewa wannan karramawa ba nasara ce ta kansa kaɗai ba, illa tunatarwa ce cewa shugabanci na gari yana ginuwa ne a kan tausayi, gaskiya, sadaukarwa da kuma hidimtawa bil’adama.
Ya yabawa masu shirya taron bisa nasarar da suka samu, yana mai cewa taron ya bai wa mahalarta darussa masu amfani kan shugabanci nagari, aikin sa-kai da ci gaban al’umma.
A cewarsa, ɗaya daga cikin manyan darussan da aka koya a taron shi ne muhimmancin haɗa kai wajen aiwatar da shirye-shiryen da ke inganta rayuwar jama’a da ƙarfafa al’umma, maimakon barin tsoro ko rashin tabbas su hana ci gaba.
Mataimakin gwamnan ya sake jaddada aniyarsa ta ci gaba da inganta ayyukan jinƙai, zaman lafiya, haɗin kai, ci gaba mai ɗorewa da ƙarfafa al’umma. Ya kuma yi alƙawarin ci gaba da haɗa kai da masu aikin sa-kai, abokan hulɗar ci gaba da sauran masu ruwa da tsaki domin inganta rayuwar marasa galihu.
Danbayo ya sadaukar da lambobin yabon ga masu aikin sa-kai, abokan aikinsa da sauran abokan hulɗa waɗanda sadaukarwarsu ga ayyukan jin ƙai ta haifar da gagarumin sauyi, yana mai jaddada cewa ana samun sauyi mai ma’ana ne ta hanyar haɗin kai da ayyukan alheri.
A ƙarshe, ya sake gode wa ƙungiyar Dangin Juna Afirka Initiative, AC4D, Gidan Alheri da duk masu goyon bayansa bisa amincewar da suka nuna masa, tare da tabbatar da cewa zai ci gaba da tsayawa kan manufar hidima sama da son kai.
