
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jami’an tsaro sun kama Adeniyi Adeyemi, wato wanda ya kira kansa da Darakta Janar na hukumar bogi ta PFIPC.
Hakan na zuwa ne bayan da Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta bayar da izinin kama shi.
Rahotanni sun bayyana cewa, an yi zargin cewa an cafke Adeyemi ne a maɓoyarsa ta Jihar Osun, inda ake sa ran kai shi Hedikwatar Rundunar ‘Yan sanda a Abuja, ranar Talata.
Babu cikakken bayani game da yadda aka kama shi a lokacin haɗa wannan rahoto.
Hakan na zuwa ne sa’o’i bayan Mai Shari’a Mohammed Umar ya umarci a kama shi sakamakon rashin halartar zaman kotu a lokuta mabanbanta fomin gurfanarwa.
An maka Adeyemi ne a kotu kan tuhume-tuhume guda takwas da suka shafi zarge-zargen bogi, damfara da sojan gona da aka shirya gabatarwa akansa.
Daga cikin shaidun da aka zayyano domin su tabbatar da zarge-zargen akansa akwai Shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, Paul Emmanuel, Jeremiah Imoukhede da kuma Ituah Sylvester. Haka kuma akwai wasu mutane biyu daga Ofishin Akanta Janar na Ƙasa.
