Ra’ayin Manhaja

Illar gurɓata muhalli ga rayuwar al’umma

Illar gurɓata muhalli ga rayuwar al’umma

Rahotanni daga Hukumar kula da lafiya ta duniya (WHO) sun nuna cewa, aƙalla gurɓata muhalli na sanadiyyar salwantar rayukan kusan mutum miliyan goma a duniya a kowace shekara. Wani babban abin tashin hankalin shi ne Nijeriya na daga cikin ƙasashen Afirika da wannan matsala ta yi ƙamari a cikinta, kuma ita ce ta huɗu a cikin jerin ƙasashen duniya da ake fama da wannan matsala ta gurɓata muhalli. Domin kuwa ƙididdiga ta nuna cewa, duk cikin ’yan Nijeriya dubu ɗari, akwai mutum ɗari da hamsin da ke mutuwa sakamakon shaƙar gurɓatacciyar iska a kowace shekara. A ƙasar Afganistan mutum 406,…
Read More
Illolin shaye-shayen ƙwayoyi da hanyoyin shawo kan lamarin

Illolin shaye-shayen ƙwayoyi da hanyoyin shawo kan lamarin

Shaye-shaye ya zama ruwan dare a tsakanin al'umma musamman ma matasa maza, wanda babban abin takaici halayya ce da aka fi dangantawa ga maza, sai ga shi ta zama ruwan dare har mata sun fi maza iyawa. Masu aure da waɗanda ba su da shi, shaye-shaye na nufin duk wani yanayin da ɗan adam zai saka kan shi don sauya yanayin tunaninsa ko nazarin shi ta yadda ba zai iya bambanta ya kamata da akasin hakan ba. A zamanin baya, muna jin labarin irin waɗannan ɗabi’un a ƙasashen ƙetare, wasa-wasa har ta shigo cikin ƙasarmu da al’ummarmu. Da yawa mutane…
Read More
Matsalar tsaro: Wa’adin shekara guda

Matsalar tsaro: Wa’adin shekara guda

A kwanakin baya ne shugaban ƙasa Ahmed Bola Tinubu ya bai wa ministocin tsaro da hafsoshin tsaron Nijeriya wa’adin shekara guda domin kawo ƙarshen duk wani nau’in rashin tsaro a ƙasar. Da yake fuskantar ƙalubalen, Ministan Tsaro, Abubakar Badaru, ya ziyarci wasu manya-manyan hafsoshin soji domin jin yadda za a ɓullo wa bakin zaren. Kafin yanzu dai an fara samun tashin hankali sakamakon yawaitar hare-haren ta'addanci da kashe-kashe a wasu sassan ƙasar inda akasarin 'yan Nijeriya suka lulluɓe cikin yanayi na firgici da damuwa. A baya-bayan nan ne dai rundunar sojin Nijeriya ta rashin kimanin mutane 37 da suka haɗa…
Read More
Yaƙi da cutar kwalara a Nijeriya

Yaƙi da cutar kwalara a Nijeriya

A cikin rahotonta na baya-bayan nan, Cibiyar Kula da Cututtuka ta Nijeriya ta sanar da jimillar mutane 19,228 da ake zargin sun kamu da cutar kwalara, ciki har da mutuwar mutane 466 a shekarar 2022. A ra'ayin wannan jarida, wannan lamari ne mai firgitarwa da ya kamata gwamnati ta ɗauki matakin daƙile shi cikin gaggawa. Kwalara cuta ce da ake saurin kamuwa da ita, kuma ta na haifar da gudawa da amai. Ana kamuwa da ita daga najasa ta hanyar gurɓataccen abinci, abin sha, da rashin tsafta, kuma ta na haifar da rashin ruwa a jikin ɗan adam. Yawan masu…
Read More
Lalata da ɗalibai a jami’o’in Nijeriya

Lalata da ɗalibai a jami’o’in Nijeriya

Ga duk mai bibiyar al’amuran da suka shafi shafin yanar gizo, ko kuma in ce harkar yaɗa labarai a qasar nan ya san yadda a ’yan watannin nan ake yawan samun koke-koken game da yadda wani Malaman Jami’o’i ke lalata da ɗalibansu don su ba da maki, ko kuma don a kai su inda ba su kai ba a harkar jarabawa. Ko ba a ce komai ba, wannan wani mummunan abu ne da za a iya cewa bai kama da hakali ba, ko kuma mu ce wani abu ne da ya zama bala’in wanda idan ba a yi hankali ba…
Read More
Matasan Nijeriya, kada ku karaya!

Matasan Nijeriya, kada ku karaya!

Kwanan nan, ƙasashen duniya sun yi bikin murnar ranar matasan duniya. Ranar 12 ga watan Agusta ne Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware ranar matasa ta duniya a shekarar 1999, kuma ita ce bikin shekara-shekara na rawar da matasa maza da mata ke takawa a cikin al'umma. Yana ba da damar wayar da kan jama'a game da ƙalubale da matsalolin da ke fuskantar matasan duniya Kowace shekara, Ranar Matasa ta Duniya ta kasance wani jigo na musamman wanda ke magance matsalolin ƙalubale da matasa ke fuskanta. Taken ranar matasa ta duniya a shekarar 2023 shi ne ‘Green Skills for Youth: Towards…
Read More
Kawar da bautar da ƙananan yara

Kawar da bautar da ƙananan yara

Akwai wani al'amari mai matuƙar tayar da hankali da ban tausayi kan yadda ake amfani da yara masu ƙananan shekaru maza da mata don yin aiki ko bauta a gidaje da sauran wurare da suka haɗa da shaguna, otel-otel, wuraren kwana na manyan makarantu ko ɗakunan kwanan ɗalibai a jami’o’i. Akasarin yaran ’yan ƙasa da shekaru 15 ne kuma ana ɗaukarsu ne da nufin yin aikace-aikacen da suka haɗa da shara, wanke-wanke, wanki, goge-goge, ɗebo ruwa da rainon jarirai da kula da yayayyun yara da makamantansu. Mafi yawan yaran ana kawo su cikin birni daga ƙauyuka lokaci zuwa lokaci, ta…
Read More
Daƙile matsalar mace-macen mata masu juna biyu a Nijeriya

Daƙile matsalar mace-macen mata masu juna biyu a Nijeriya

Matsalar mace-macen mata da yara a lokacin ciki ko haihuwa dai ta jima ta na ci wa ƙasashe masu tasowa tuwo a ƙwarya. Alal misali, ƙasashen da suka ci gaba mata 7 zuwa 15 ne ke mutuwa a cikin mata masu juna 100,000 daga lalurar ciki ko haihuwa; amma a ƙasashe masu tasowa har wajen mata 100-300 ne kan rasu sanadiyyar lalurorin ciki ko haihuwa. Wani sabon rahoton da hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya suka fitar na cewa a duk minti biyu mace na mutuwa a duniya yayin da take ɗauke da juna biyu ko haihuwa. Hakan na ƙara nuna rashin…
Read More
Yaƙi da cutar mantuwa a Nijeriya

Yaƙi da cutar mantuwa a Nijeriya

Wani bincike na masana ya nuna cewa ’yan Nijeriya na cikin waɗanda suka fi fama da ciwon mantuwa a duniya. Ciwon mantuwa da ake kira ‘dementia’ na ɗaya daga cikin cututukan da ke barazana ga lafiyar bil’adama a duniya. Wata ƙungiyar da ta gudanar da binciken mai suna 'Alzheimer’s Disease International' ta ce, sama da mutum miliyan 40 ke fama da cutar a duniya ba tare da sun sani ba. Binciken ya kiyasta cewa kashi 75 cikin 100 na ɗauke da cutar ba tare da sun sani ba, kuma waɗannan alqaluma sun fi yawa a ƙasashen Nijeriya da Indiya da…
Read More
Magance matsalar rashin tsaro a Filato da sauran jihohi

Magance matsalar rashin tsaro a Filato da sauran jihohi

A kwanakin baya ne Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci jami’an tsaro da su gaggauta gurfanar da waɗanda suka aikata kisan gilla a wasu sassan jihohin Filato da Binuwai. Shugaban ya kuma bayyana tashe-tashen hankula a jihohin biyu a matsayin abin takaici. Baya ga haka, ya kamata jami’an tsaro su dakatar da tashe-tashen hankula a yankin Arewa maso Yamma da Kudu maso Gabas da sauran sassan ƙasar nan. Mummunan hare-haren da aka kai a Jihohin Filato da Binuwai sun haddasa asarar rayuka da lalata gidaje. Tun a ranar 15 ga watan Mayu ne aka fara zubar da jini a…
Read More