Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tsare-tsaren Tattalin Arziki na ƙasa, Taiwo Oyedele, ya bayyana abin da mutane da dama suka riga suka fahimta lokacin da ya shaida wa manema labarai a wajen Taron Shugabannin Kamfanoni na Afirka da aka gudanar a Kigali na ƙasar Rwanda cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na taka rawar gani wajen tallata Nijeriya ga masu zuba jari na duniya.
“Abin farin ciki game da Shugaban ƙasa shi ne bai gajiya wajen tallata Nijeriya ba. Shi ne babban mai tallan ƙasar nan,” inji Oyedele.
Tun bayan hawansa mulki, Shugaba Tinubu ya ɗauki Nijeriya zuwa gaban masu zuba jari na duniya ta hanyar da ba a saba gani ba. Ya rungumi dabaru daban-daban wajen nuna wa duniya cewa Nijeriya na da damar zuba jari mai fa’ida.
ɗaya daga cikin dabarun shi ne gudanar da rangaɗin cibiyoyin tattalin arzikin duniya domin jawo hankalin masu zuba jari na ƙetare. Hakan ya sa Tinubu ya zama shugaban Afirka na farko da ya buga kararrawar rufe kasuwa a NASDAƙ da ke birnin New York, wadda ita ce kasuwar hada-hadar hannayen jari ta farko da ake gudanarwa ta hanyar lantarki a duniya.
A taron Shugabannin Kamfanoni na Afirka da aka gudanar kwanan nan a Kigali, shugaban ƙasar ya sake amfani da damar wajen bayyana wa duniya sauye-sauyen tattalin arzikin Nijeriya da kuma damar kasuwanci da ke cikinta.
Wani muhimmin ginshiƙi na wannan yaƙin neman masu zuba jari shi ne gyaran tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ta aiwatar. Bayan makonni kaɗan da rantsar da shi a ranar 29 ga Mayun 2023, shugaban ƙasar ya umarci Babban Bankin Nijeriya (CBN) da ya haɗa farashin canjin kuɗi zuwa tsari guda.
Tun kafin wannan lokaci, Bankin Duniya da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) sun sha sukar tsarin farashin canji iri-iri da Nijeriya ke amfani da shi, wanda suka ce ya cika da damfara da cin hanci.
Rahotanni sun nuna cewa wasu jami’an CBN ba su son a haɗa tsarin saboda anfani da suke samu daga tsohon tsarin. Sai dai Shugaba Tinubu ya kawo ƙarshen wannan jan ƙafa ta hanyar bai wa babban bankin umarnin aiwatar da sauyin.
Wannan mataki ya haifar da gagarumin sauyi a kasuwar canjin kuɗi, inda ya rage damfara da ake yi ta hanyar sauya dala ba bisa ƙa’ida ba, tare da fara daidaita darajar naira da kuma jawo hankalin masu zuba jari na ƙasashen waje.
Haɗa tsarin canjin kuɗin ya kuma rage damar da wasu shugabannin bankuna ke amfani da ita wajen anfani da giɓin farashin canji domin samun riba ta haramtacciyar hanya, yayin da hakan ya ba CBN damar kula da kasuwar kuɗi yadda ya kamata.
Haka kuma, Shugaba Tinubu na anfani da gyaran da aka yi wa Kasuwar Hannayen Jari ta Nijeriya (NGX), wadda ta zama ɗaya daga cikin kasuwannin jari mafi riba a duniya.
Sauye-sauyen da aka aiwatar sun sa masu zuba jari na ƙasashen waje suka fara tururuwar saka kuɗaɗensu a kasuwar. A shekarar 2025 kaɗai, masu zuba jari daga ƙetare sun zuba fiye da dala biliyan 20 a NGX.
Dalilin wannan tururuwa kuwa ba shi da wahalar ganewa. Matsakaicin ribar jarin da ake samu a NGX ya kai kusan kashi 40 cikin ɗari a shekara, wanda yake ɗaya daga cikin mafi girma a kasuwannin duniya.
Bugu da ƙari, farashin hannayen jari da dama a kasuwar na tashi cikin sauri, inda wasu suke ƙaruwa da sama da kashi 60 cikin ɗari cikin watanni kaɗan.
Masu zuba jari na ƙetare na cin gajiyar kasuwar ta hanyoyi biyu — suna samun babbar riba daga hauhawar farashin hannayen jari bayan sun sayar, sannan kuma suna cin moriyar kuɗin rabon riba da kamfanoni ke biya.
Kamfanin Siminti na Dangote ya biya mafi girman ribar hannun jari a shekarar 2025 da naira 45 ga kowane kaso, yayin da simintin BUA ya biya naira 10. Haka kuma, Bankin GTB ya kafa sabon tarihi a ɓangaren bankuna da rabon naira 12.76 ga kowane kaso.
Sakamakon hakan ya sa farashin hannun jarin GTB ya tashi daga naira 126 a ranar 28 ga Afrilu, 2026 zuwa naira 147 a ƙarshen makon da ya gabata.
Wani babban abin da ke nuna ƙarfin NGX shi ne yadda ƙimar kasuwar ta ƙaru da sama da naira tiriliyan 40 cikin watanni huɗun farko na shekarar 2026. A wata rana ta watan Mayu 2026 ma, ƙimar kasuwar ta ƙaru da naira tiriliyan 5 cikin rana guda.
Duk waɗannan nasarori na daga cikin abubuwan da ke sauƙaƙa wa Shugaba Tinubu tallata Nijeriya ga masu zuba jari na duniya.
Har ila yau, gyaran tsarin haraji da gwamnatin Tinubu ta fara aiwatarwa na daga cikin muhimman abubuwan da shugaban ƙasar ke anfani da su wajen jawo hankalin masu zuba jari.
Ana sa ran gyaran harajin zai taimaka wajen ƙara kaso na harajin da ake tarawa idan aka kwatanta da girman tattalin arziƙin ƙasar. Nijeriya yanzu na fatan kaiwa kaso 15 cikin ɗari a gajeren lokaci, sannan daga baya zuwa kaso 18 cikin ɗari, sabanin kaso 10 cikin ɗari da ake samu a baya.
Kuɗaɗen da gwamnati za ta samu daga wannan gyara za su taimaka wajen sake gina manyan ababen more rayuwa, wanda hakan zai ƙara jawo masu zuba jari kai tsaye daga ƙasashen waje.
Nasarar da Tinubu ke samu wajen tallata Nijeriya na da alaƙa da yadda sauye-sauyen da ya aiwatar suka mayar da ƙasar wata kyakkyawar kasuwa mai jan hankali.
Haka kuma, ƙaruwar ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje da Nujeriya ta samu a baya-bayan nan na bai wa masu zuba jari tabbacin cewa za su iya mayar da ribarsu zuwa ƙasashensu cikin sauƙi — wani muhimmin abin dubawa ga masu zuba jari na duniya.
Jaridar Blueprint Manhaja na yaba wa Shugaba Tinubu kan ƙwarewarsa wajen tallata Nijeriya ga duniya, tare da yi masa fatan ƙarin nasara a ƙoƙarinsa na bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.
