Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Rahotanni sun bayyana cewa kamfanin Meta ya shiga cikin cece-kuce bayan da ya sallami dubban ma’aikata, tare da zuba jari mai yawa wajen ɗaukar ƙwararren masani a fannin fasahar ƙirƙirar basira ta na’ura mai kwakwalwa, wato Artificial Intelligence (AI).
Rahotannin da suka bazu a kafafen sada zumunta sun nuna cewa kamfanin ya sallami kusan ma’aikata 8,000 a rana guda da kuma ƙaddamar da sabon tsarin AI ɗinsa mai suna Muse, lamarin da ya haddasa muhawara kan yadda fasahar AI ke ƙara maye gurbin ayyukan mutane.
Mutane da dama a shafukan sada zumunta sun bayyana cewa wannan wani sabon misali ne na yadda fasahar AI ke korar ma’aikatan ɗan Adam. Sai dai wasu kuwa sun yi hujjar cewa lamarin ya fi nuna sauyin irin ƙwarewar da manyan kamfanonin fasaha ke nema, ba wai kawar da ma’aikata gaba ɗaya ba.
Muhawarar ta ƙara zafi ne bayan da rahotanni suka bayyana cewa shugaban Meta, Mark Zuckerberg, ya ɗauki Andrew Tulloch, ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa kamfanin Thinking Machines Lab, a wata yarjejeniya da ake zargin ta kai dala biliyan 1.5.
Rahotannin sun kuma ce kamfanin Andrew Tulloch ya kai kimar kusan dala biliyan 12 duk da cewa har yanzu bai fitar da wani samfurinsa a hukumance ba.
Masana da masu sharhi sun bayyana cewa kamfanonin fasaha irin su Meta na ƙara bai wa ƙwararrun masu ilimin AI muhimmanci, lamarin da ya sa ake matuƙar neman injiniyoyin AI da masu kula da kayayyakin AI fiye da wasu tsofaffin ayyukan fasaha.
A gefe guda kuma, rahotanni sun nuna cewa ma’aikatan da abin ya shafa za su samu albashin sallama na makonni 16 bayan korarsu daga aiki.
Wane ne Andrew Tulloch?
Andrew Tulloch mai shekaru 35 ƙwararren injiniya ne a fannin Artificial Intelligence da Machine Learning, wanda aka fi sani da kasancewa ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa Thinking Machines Lab. A tsawon shekarunsa na aiki, ya yi aiki a manyan kamfanonin fasaha ciki har da OpenAI da kuma Meta.
A watan Oktoban 2025 ne Tulloch ya koma Meta bayan barinsa daga Thinking Machines Lab.
Mista Andrew Tulloch ya yi karatun digirinsa na farko a jami’ar Sydney tsakanin shekarar 2007 zuwa 2011, inda ya kammala digiri a fannin Adɓanced Mathematics tare da ƙwarewa a fannin ilimin lissafi da ƙididdiga, wato Mathematics da Statistics.
Ya kammala karatunsa da darajar First Class Honour tare da samun lambar yabo ta jami’ar Medal, wadda ake bai wa ɗalibin da ya fi kowa ƙwazo a Faculty of Science.
Bayan haka ya tafi Uniɓersity of Cambridge daga 2013 zuwa 2014, inda ya samu digiri na biyu a fannin Mathematical Statistics tare da ƙwarewa a Statistics da Machine Learning.
