Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Jam’iyyar APC ta tabbatar da Hon. Abdullahi Yahaya Tsamiyar Kara a matsayin ɗan takararta na kujerar Majalisar Jihar Kano mai wakiltar ƙaramar hukumar Gezawa a zaɓen 2027.
Wakilan jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Ahmad Haruna Bichi tare da jami’an uwar jam’iyyar APC ta jihar Kano, wakilan hukumar zaɓe ta ƙasa, jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki ne suka shaida tabbatar da takarar tasa. An gudanar da taron ne ranar Laraba a harabar sakatariyar APC ta Gezawa.
Da yake jawabi bayan tabbatar da shi, Hon. Tsamiyar Kara ya gode wa Allah bisa wannan nasara tare da bayyana ranar a matsayin rana ta farin ciki da nuna goyon baya daga al’umma.
Ya kuma gode wa al’ummar ƙaramar hukumar Gezawa bisa soyayya da goyon bayan da suke ba shi, tare da yaba wa jagoran APC na Gezawa, Murtala Zainawa, da sauran shugabannin jam’iyyar bisa gudunmawar da suka bayar wajen ganin an samu nasara.
Hakazalika, ya yaba wa shugabancin APC na jihar Kano bisa yadda suka gudanar da zaɓen fidda gwani cikin lumana da kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba a faɗin jihar.
Hon. Tsamiyar Kara ya kuma yaba wa gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa nuna dattako, jagoranci da ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya a jihar. Ya ce jajircewar gwamnan ta taimaka wajen gudanar da zaɓen cikin adalci da lumana.
Ya yi addu’ar Allah Ya tabbatar da Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin zababben gwamnan Kano tare da ba shi damar komawa karo na biyu, sannan Allah Ya ba su nasarar sake lashe kujerar Majalisar Jiha ta Gezawa.
Tsamiyar Kara ya ce tun farko ya gudanar da siyasa cikin mutunci da biyayya ga jam’iyya ba tare da zagin kowa ko cin mutunci ba, yana mai kira ga sauran waɗanda suka fafata da shi da su haɗa kai domin cigaban jam’iyyar APC.
Ya jaddada cewa babban burinsu shi ne ganin APC ta samu nasara a dukkan matakai, yana mai tabbatar da cewa za su ci gaba da biyayya da aiki tukuru domin cigaban jam’iyyar.
A ƙarshe, ya gode wa magoya bayan APC da al’ummar Gezawa bisa amincewar da suka nuna masa, tare da alƙawarin yin aiki domin tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a Gezawa, jihar Kano da ƙasa baki ɗaya.
