
Wasu mazauna Jihar Borno sun bayyana damuwa kan abin da suka bayyana a matsayin rashin nuna kulawa iri ɗaya daga Gwamnatin Tarayya bayan awon-gaba da ɗalibai 42 na firamare da ƙaramar sakandare daga ƙauyen Mussa da ke Karamar Hukumar Askira Uba, inda suka ce martanin gwamnati ya fi bayyana a wani makamancin lamarin da ya faru a Jihar Oyo.
Rahotanni sun bayyana cewa Shugaban Cibiyar Ƙungiyoyin Fararen Hula ta Jihar Borno, Abubakar Suleiman, ya ce yayin da gwamnatin tarayya ta tura manyan jami’ai ciki har da Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Akan Harkar Tsaro da Ministan Tsaro zuwa Oyo bayan sace ɗalibai da malamai a can, ba a ga irin wannan ziyara ko mataki a Borno ba duk da hare-haren sace mutane da aka samu a yankin.
Haka kuma, wani mai sharhi akan harkokin siyasa a jihar, Abubakar Kareto, ya ce sace ɗaliban Askira Uba da kuma lamarin Oyo sun nuna yadda makarantu a yankunan karkara ke cigaba da kasancewa cikin haɗari.
Ya yi zargin cewa martanin da aka gani a Oyo ya fi karfi da bayyana a fili idan aka kwatanta da abin da aka gani a Borno, lamarin da zai iya haifar da jin an yi watsi da wasu al’ummomi.
A nasa ɓangaren, shugaban ƙungiyar matasan Kudancin Borno, Samaila Kaigama, ya buƙaci mahukuntan jihar da na tarayya su ƙara himma wajen ceto ɗaliban da aka sace, yana mai cewa iyalan waɗanda abin ya shafa na buƙatar tabbaci da bayanai kan matakan da ake ɗauka domin dawo da su gida lafiya.
Saidai, wata majiya daga fadar shugaban ƙasa ta musanta zargin da ke cewa Gwamnatin Tarayya ta fifita lamarin Oyo akan na Borno.
A cewarta, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sha ambaton duka lamurran biyu a taruka da bayanan tsaro, tare da jaddada cewa hukumomin tsaro na bai wa kowanne daga cikin su muhimmanci iri ɗaya.
Majiyar ta kuma bayyana cewa bambancin da aka gani a yadda jama’a da kafafen yaɗa labarai suka mayar da hankali kan lamarin Oyo ya samo asali ne daga wasu dalilai da suka haɗa da yawan rahotanni da bidiyoyin da suka bazu a kafafen sada zumunta.
Saboda haka, hakan ba ya nufin akwai wani bambanci a matakin da gwamnati ke ɗauka wajen ceto waɗanda aka sace a jihohin biyu ba, saidai tana bin matakan da suka dace wajen ganin an samu nasara a kowane ɓangare.
