Mu kula da yanayin mata domin rashin fahimtarsu na jawo mutuwar aure

Spread the love

Assalamu alaikum, barka da warhaka, Edita. Da fatan kowa yana lafiya.

A lokuta da yawa aure yakan mutu saboda rashin sani ko ƙarancin ilimin maza game da yanayin mata a lokacin da za su fara al’ada (menstruation), ko suke yi; ko lokacin da suke ɗauke da ƙaramin ciki, wato lokacin laulayi da lokacin da cikin ya kai wata bakwai zuwa lokacin da za su haife shi.

Kwana 5 ko 8 kafin su fara al’ada suna zama kwanakin haƙuri ga duk magidancin da ya gane haka.

Duk da yake cewa ba a cika tattauna irin waɗannan abubuwa a nan ƙasar Hausa ba, amma ya kamata mu fara domin fahimtar juna da rage matsalolin da suke kaiwa ga mutuwar aure.

Na taɓa karanta cewa mata na fama da wani yanayi mara daɗi kafin zuwan jinin al’ada da Bature ke kira da ‘premenstrual syndrome’.

Wannan yanayi yakan sa su jin gajiya mai yawan gaske, ko su riƙa jin fushi kaɗan-kaɗan wanda zai iya kaiwa ga kuka kan matsala ƙarama; kuma sukan samun abin da ake cewa ‘mood swings,’ wato canjin yanayi nan da nan, daga farin ciki zuwa baƙin ciki.

Wannan yanayin da na ambata a baya da suna PMS ɗin yakan girma ga waɗansu matan har ya zama wani yanayi da ake kira PMDD, wato ‘Premenstrual Dysphoric Disorder’.

Wannan ya fi matsala domin yakan sanya su fishi mai kama da cutar damuwa (depression).

Wani lokacin sukan yi kuka ba gaira ba dalili, ko su shiga damuwa saboda jin cewa kamar kowa ya tsane su, ko kuma su samu kansu a yanayin raguwa ko ƙaruwar son cin abinci, ko rashin jin daɗin jiki gaba ɗaya ko ciwon kai ko ciwon mara da ciwon kan mama.

Macen da ke fama da PMDD takan sha wahala kafin tashi daga inda take a kwance ko zaune.

Tana kasa mayar da hankali kan kowane abu, kuma takan yi fushi babu dalili, don haka ta ke faɗa da kowa har mijinta, ta yi ta ihu ga ’ya’yanta ko ɗalibanta, ko ma tai ta jibgarsu kan laifi ɗan kaɗan.

A irin wannan hali, matuƙar maigida zai ce a’a ga wata buƙatarta, to za ta iya kwana tana kuka, kuma za ta iya faɗa masa komai ya zo bakinta.

Irin wannan ta sa in ka yi aure ake ce maka ka yi haƙuri. Nasihar ke nan duk inda ka je!

To babu maganin wannan matsalar ne?

Gaskiya ni dai ba likita ba ne, amma na karanta wasu shawarwari da likitoci ke bayarwa don rage zafin matsalar.

Likitocin sukan ce wa mace ta sha ‘antidepressants’, wato magunguna da ke rage damuwa wato ‘depression’.

Hakana sukan cewa mace ta guji zuwa shagulgulan biki ko shiga cikin mutane a lokacin.

Bugu da ƙari, a kan ba su shawara da su riƙa cin abinci mai gina jiki a lokacin tare da yin wasu abubuwa da za su motsa jikinsu wato ‘edercise’ sosai ko iya iyawarsu.

Wannan shawarwari ba ga magidanta kaɗai suka takaita ba, saƙo ne har ga iyaye da suke da ’ya’ya matan da aka kasa gane matsalarsu.

Ga wacce ta fahimci tana fama da irin wannan yanayin, to ina ba ta shawara da ta tattauna matsalar da mijinta don faɗakar da shi.

Wassalam.

Daga MUSTAPHA MUSA MUHAMMAD. 09123302968.

By ukarofi

Leave a Reply