Alhaji Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu)
Ni ne Emmanuel Hayanchi, ɗan asalin ƙaramar Hukumar Zuru, daga unguwar Road Block. Asalina ɗan Zuru ne tun daga kakannina har zuwa iyaye na.
Dalilin rubuta wannan wasiƙa shi ne na bayyana goyon bayana da biyayyata ga gwamnatin ka a matsayin Gwamnan Jihar Kebbi, tun daga yanzu har zuwa shekarar 2027, In Sha Allah. Ni matashi ne mai kishin ƙasa, musamman ma jihata ta Kebbi, kuma ina da niyyar tsayawa takarar kansila a Zuru Ward a ƙarƙashin jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
Burina shi ne na yi koyi da kyawawan halayen Ka na shugabanci, musamman wajen taimakon talakawa, kare rayukansu da dukiyoyinsu, har ma da sadaukarwa idan hakan ya zama dole.
Haka kuma, ina amfani da wannan dama wajen wayar da kan ’yan uwana, musamman daga bangaren addinin Kirista, cewa siyasa ba addini ba ce.
Ya kamata mu fahimci cewa bambancin addini da kabila bai kamata ya raba mu ba, sai dai ya zama hanyar gina haɗin kai domin ci gaban ƙasar mu ta gado. Wasu mutane na kuskuren fahimtar siyasa da addini, alhali hakan ba gaskiya ba ne.
Jam’iyyar APC jam’iyya ce ta kowa da kowa — Musulmi, Kirista, har ma da waɗanda ba su da wani addini. Allah Ya ƙara wa Jagoranmu, Mai Girma Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu) lafiya, nisan kwana, da ɗaukaka. Amin.
Ni dai matashi ne mai shekaru 24, amma ina da matuƙar kishin ƙasata Nijeriya, jihata Kebbi, da ƙaramar hukumar Zuru, kamar yadda Mai Girma Gwamna yake nuna kishinsa gare su. Haka nima ina ƙoƙarin yin koyi da shugabancinsa.
Lambar waya: 08134514854
Imel: [email protected].
