Nijeriya ba za ta rushe ba duk da ƙalubalenta – Gowon

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Tsohon Shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Yakubu Gowon mai ritaya, ya bayyana cewa Nijeriya ba za ta rushe ba duk da irin ƙalubalen siyasa, tattalin arziki da matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta a halin yanzu.

Gowon ya bayyana hakan ne ranar Talata a Abuja yayin ƙaddamar da littafin tarihin rayuwarsa mai shafi 859 mai taken My Life of Duty and Allegiance.

Tsohon shugaban ƙasar, wanda ya cika shekaru 91 a watan Fabrairu, ya kuma gargadi ƴan siyasa kan abin da ya kira siyasar “a mutu ko a yi rai,” yana mai cewa rashin gudanar da sahihin zaɓe har ma da zaɓukan cikin jam’iyya na ci gaba da hana dimokuraɗiyyar Nijeriya bunƙasa.

“Dole ne mu dakile irin siyasar son rai da ƴan siyasa ke yi wadda suke kira siyasar do-or-die, da kuma gazawar gudanar da sahihin zaɓe ko da kuwa na cikin jam’iyya ne,” in ji Gowon.

Ya ƙara da cewa bai kamata ‘yan Nijeriya su yarda masu suka su ɗora wa ƙasar tambarin ƙasa mai gazawa ba.

“Lokacin da nake shugabanci ƙasar ba ta rushe ba, kuma ina da yaƙinin cewa duk da ƙalubalen da ake ciki yanzu, Nijeriya ba za ta rushe ba,” inji shi.

Gowon ya bayyana damuwarsa kan yadda ‘yan Nijeriya ke rikita ƙananan matsaloli da mafita masu wahala.

“Abin da ke damuna shi ne yadda ‘yan Nijeriya ke kawo mafita masu wahala ga matsaloli masu sauƙi, sannan su ƙara rikita lamarin da wasu hanyoyi masu sarkakiya da ke haddasa tashin hankali,” ya ce.

Gowon ya mulki Nijeriya tsakanin 1966 zuwa 1975, lokacin da aka yi yaƙin basasa daga 1967 zuwa 1970 kafin daga bisani gwamnatin sa ta fara aikin sake gina ƙasa bayan yaƙin.

A wajen taron, tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan da tsohon ministan tsaro Janar Theophilus Danjuma sun yabawa Gowon bisa shahararriyar furucinsa na “ba mai nasara, ba wanda aka ci,” bayan yaƙin basasa.

Jonathan ya bayyana littafin tarihin a matsayin wata muhimmiyar shaida ta tarihin Nijeriya.

“Wannan ba kawai ƙaddamar da littafi ba ne, a’a gabatar da wata rayayyar shaida ce daga wani shugaba da ya taka muhimmiyar rawa a tarihin ƙasa,” in ji Jonathan.

Ya ce littafin ya ƙunshi darussa masu muhimmanci kan shugabanci, sasanci, zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.

Jonathan ya kuma yabawa Gowon bisa kafa shirin bautar ƙasa na NYSC wanda ya ce ya taimaka wajen haɗa kan matasan Nijeriya tare da samar da malamai ga makarantu musamman a yankunan karkara.

“Ina tuna lokacin da nake aji uku a sakandare a shekarar 1973 lokacin da masu yi wa ƙasa hidima suka zo makarantar mu. Sun koya mana darussa kamar lissafi, sinadarai da kimiyyar halittu,” inji Jonathan.

Shi ma Danjuma, ta bakin tsohon shugaban hafsoshin tsaro Janar Martin Luther Agwai, ya yabawa Gowon kan yadda ya jagoranci ƙasar a lokacin yaƙin basasa.

Ya ce furucin “ba mai nasara, ba wanda aka ci” ya taimaka wajen samar da sulhu da sake haɗa kan Nijeriya bayan yaƙin.

Taron ya samu halartar manyan baƙi da suka haɗa da tsohon shugaban mulkin soja Ibrahim Babangida ta hannun ‘yarsa Aisha Babangida, shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ta hannun Sanata Ireti Kingibe, Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III, Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume da shugaban kotun ɗaukaka ƙara Monica Dongban-Mensem.

A yayin taron, Janar Danjuma ya bayar da gudummawar naira biliyan uku domin sayen kwafe 12 na littafin ga jami’o’i 20 da suka bai wa Gowon digirin girmamawa.

Shugaban kamfanin Dangote Group, Aliko Dangote, ya bayar da naira miliyan 500, yayin da shugaban BUA Group Abdul Samad Rabiu ya sayi kwafe na littafin na naira miliyan 25.

By ukarofi