Abin da ya sa ba zan zama daraktan yaƙin neman zaɓen APC ba – Wike

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan Abuja Nyesom Wike, ya bayyana dalilin da ya sa ba zai karɓi muƙamin Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC ba domin zaɓen 2027 duk da goyon bayansa ga Shugaba Tinubu.

Wike ya bayyana haka ne a ranar Asabar bayan wata ziyarar sanya ido da ya kai a wuraren wasu ayyukan titi guda biyu a Abuja, inda ya bayyana gamsuwa da salo da ƙwarin aikin ‘yan kwangilar.

Ya ce, matakin nasa na da alaƙa da darussa da ya samu daga zaɓukan baya, inda ya ce da dama daga cikin waɗanda suka riƙe muƙamin su kan faɗi a kujerunsu na gida.

Ya bayar da misali da tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, wanda ya riƙe muƙamin darakta-janar na yaƙin neman zaɓen Marigayi Muhammadu Buhari a zaɓen 2015 amma kuma ya rasa Jihar Ribas.

Wike ya ce, irin hakan ya sake faruwar da Amaechi a matsayinsa na daraktan yaƙin neman zaɓen a 2019, yayin da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya faɗi a jihar Kwara.

Ya ƙara da cewa, Aminu Waziri Tambuwal, tsohon gwamnan Sakkwato, wanda ya yi wa Atiku Abubakar darakta-janar na yaƙin neman zaɓe a 2023, ya faɗi a zaɓe a Jihar Sakkwato. Shi ma tsohon gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong da ya jagoranci na APC a shekarar, ya faɗi a jiharsa.

A cewar Ministan Abujan, babban burinsa shi ne ya tabbatar da cewa shugaba Tinubu ya yi nasara a Abuja da Jihar Ribas a madadin karɓar wani muƙamin yaƙin neman zaɓe.

Har ila yau, Wike ya jaddada cewa shi ba ɗan jam’iyyar APC ba ne, saidai ya gamsu da goya wa Shugaba Tinubu baya kan tsare-tsaren siyasa da salon mulkinsa, yana mai bayar da misali da ɗan takarar kujerar sanatan Kwara ta Tsakiya a jam’iyyar PDP a zaɓen 2027, Saliu Mustapha, wanda yake goyon bayan Tinubu a matakin ƙasa.

By Babaji

Leave a Reply