
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A safiyar yau Asabar ne Dakta Ibrahim Mohammed Fadul da aka fi sani da Imam Abuya ya rasu.
Marigayin, wanda shi ne babban Limamin Masallacin Cibiyar Anas Bin Malik Islamic da ke yankin rukunin gidajen AMSSCO Platinum City a Galadimawa, ya rasu ne a Abuja bayan fama da wani rashin lafiya.
An kuma shirya gudanar da jana’izarsa da misalin ƙarfe 1:30 na rana a Babban Masallacin Ƙasa da ke yankin Central Area a babban birnin.
Allah SWT ya jiƙansa ya kuma gafarta masa kurakuransa tare da bai wa makusantansa haƙurin juriya ga rashinsa.
