Dalilin da ya sa El-Rufai ya maka ICPC a kotu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya maka Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, bisa zargin hana shi ganin iyalansa yayin da yake tsare a hannun hukumar.

A cikin ƙarar da lauyansa, Ubong Akpan, ya shigar a ranar 13 ga Agusta, 2026, El-Rufai ya ce ICPC ta hana matarsa, Aichatou Asabe, da ɗansa, Abba El-Rufai, ziyartarsa.

Tsohon gwamnan ya ce matakin ya tauye masa haƙƙin samun kulawa da hulɗa da iyalansa yayin da yake tsare.

Ya kuma yi zargin cewa hana shi hulɗa da iyalansa ya hana shi samun abinci, magunguna da sauran muhimman abubuwan da iyalansa ke kawo masa.

El-Rufai ya ce an ɗauki matakin ne ba tare da wani sahihin dalili na doka ko umarnin kotu ba.

Saboda haka, tsohon gwamnan na neman kotu ta ayyana cewa matakin ICPC ya tauye masa haƙƙoƙin ɗan Adam da Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya ba shi.

Baya ga haka, El-Rufai na neman a biya shi diyyar naira biliyan 10 kan abin da ya bayyana a matsayin tauye masa haƙƙinsa.

By ukarofi

Leave a Reply