Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Masanin kimiyyar siyasa da tattalin arziki, Abbati Baƙo, ya yi kira ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da ya sake duba shirin kafa kamfanin jirgin saman da gwamnatin jihar za ta mallaka.
Abbati Baƙo ya yi wannan kiran ne a cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da ya aikewa Gwamnan Kano, inda ya bayyana cewa jihar na buƙatar mayar da hankali kan muhimman abubuwan more rayuwa da jin daɗin al’umma, maimakon gwamnati ta shiga harkar gudanar da kasuwancin sufurin jiragen sama.
Ya ce Kano za ta iya samun ci gaba sosai, amma ya kamata ta yi hakan ne ta hanyar amfani da ƙarfin kamfanoni masu zaman kansu, ba tare da ɗora nauyin jarin kasuwanci a kan gwamnatin jihar ba.
A cewarsa, ya kamata Gwamnatin Kano ta samar da kyakkyawan yanayi na kasuwanci, tsaro, filayen aiki, abubuwan more rayuwa da manufofin da za su jawo hankalin masu zuba jari, yayin da kamfanoni masu zaman kansu za su ɗauki nauyin jarin kasuwanci da haɗarinsa.
Abbati Baƙo ya yi gargadin cewa shiga harkar kasuwanci kai tsaye na iya karkatar da kuɗaɗen gwamnati daga muhimman fannoni kamar kiwon lafiya, ilimi, tsaro, ruwa da sauran ababen more rayuwa da al’umma ke buƙata.
Ya ce tarihin Kano ya nuna cewa ’yan kasuwa masu zaman kansu sun taka muhimmiyar rawa wajen gina ƙarfin tattalin arzikin jihar, inda ya kawo misalan Alhassan Dantata, Sheikh Isyaku Rabiu, Aminu Dantata, Aliko Dangote da Abdulsamad Rabiu, da sauran ’yan kasuwa da dama.
Abbati ya jaddada cewa rawar da gwamnati ya kamata ta taka ita ce samar da yanayi mai kyau da zai bai wa kamfanoni masu zaman kansu damar zuba jari da bunƙasa harkokin kasuwanci, maimakon gwamnati ta zama mai gudanar da irin waɗannan sana’o’i kai tsaye.
